Daya daga cikin 'yan majalisun tarayya masu kare muradin shugaban kasa Muhammadu Buhari a majalisar tarayya, Honarabul Yaya Bauchi Tongo ya bayyana cewa shi da takwarorin sa na majalisa masu kare martabar Buhari ba za su taba bari a ci zarafinsa ko ci masa fuska a majalisa ba.
Honarabul Yaya Tongo, wanda yake wakiltar kananan hukumomin Gombe, Funakaye da Kwami dake jihar Gombe, ya kara da cewa ba komai ya sanya suke kare muradun shugaba Buhari ba a majalisa illa kyawawan manufofi da kudirorin da yake da su ga Nijeriya da al'ummarta.
"Ko don ingataccen tsaro da aka samu a kasar nan, musamman a yankin Arewa maso gabas da ake fama da rikicin Boko Haram, ya zama wajibi mu marawa Buhari baya.
"A baya ba ma iya shiga cikin cinkoson jama'a a Arewacin kasar nan, saboda fargabar tashin bam, amma cikin ikon Allah Buhari ya zama silar kawo karshen wannan fargaba", inji Honarabul Yaya Tongo.
Dan majalisar wanda ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da RARIYA, ya kara da cewa ko don wadannan hujoji ya zama wajibi su ci gaba da kare muradun Buhari tare da mara masa baya a majalisa. Kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba akan hakan.