Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin shugaban ta Muhammadu Buhari a ranar Litinin din da ta gabata 4 ga watan Yuni ta bayar da umurin hana shan shisha a dukkanin wuraren gwamnati.
Haka ma ministan lafiya a kasar Farfesa Isaac Adewole ya bayar da umurni ga dukkan jami'an tsaro da su cafke dukkan wanda suka samu ya karya dokar.
NAIJ.com ta samu cewa ministan lafiyar ya bayar da wannan umurnin ne a wajen wani taro a garin Abuja don tunawa da ranar 'Hana shan sinadarin Tobacco' na duniya.
A wani labarin kuma, Kamar yadda muke samun labari daga majiyoyin mu, alkalin wani babbar kotu a jihar Oyo Mai shari'a ML Owolabi ya ranar Litinin din da ta gaba ya yi mursisi ya hana bukatar da tsohon gwamnan jihar Otunba Adebayo Christopher Alao-Akala ya shigar a gabanta bisa ga shari'ar da yakeyi da hukumar EFCC.
Shi dai tsohon gwamnan, kamar yadda muka samu, ya shigar da wata kara ce a gaban kotun koli ta kasa yana kalubalantar shari'ar da ake yi masa kuma yanzu haka yana jiran tsammanin hukunci daga gare su.
Source :naij hausa