Babban jigon arewa kuma shugaban kungiyar dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya bukaci a nuna masa wani aiki daya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala a shekaru uku da ya kwashe akan karagar mulki.
Ya kuma nemi sanin adadin mutanen da aka yankewa hukunci akan tuhumar rashawa a shirin yaki da rashawan da shugaban kasar ya kaddamar.
Yakasai yayi zargin cewa har yanzu Buhari ya gaza hukunta tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal wanda aka kama dumu-dumu da laifin rashawa.Yakasai ya bayyana cewa tsayarwarsu zai kasance akan manufofin yan takara ba wai sanayar halayensu ba,” jaridar Punch ta ruwaito.
Yakasai ya bayyana cewa a baya Yan Najeriya sunyi kuskure, daga tsohon shugaban kasa Olusegun zuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen zabar hallaya ba wai ingancin shirye-shiryen da yan takarar suka tanadar ba.
Source :naij hausa