Kakakin rundunar ‘yansadar jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya bayyana haka a birnin Gusau, inda ya ce, jami’an su sunyi musayar wuta da wasu ‘yanbindiga da akan babura kafin suka tsere cikin daji.
Yace, ‘jami’an su sun yi nasarar kama daya daga cikin ‘yan bidigan, tare da kwace muggan makamai daga hannunsa.
Wani rahoto da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar ya nuna cewa daga shekara 2011 zuwa yanzu, ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 1,221 yayin da suka jikkata mutanen 1,781.
Kakakin majalisar dokokin na jihar Zamfara, Alhaji Sanusi, ya ce 'yan bindiga sun sace shanu akalla 8,000 da lalata gonaki da kuma rusa gidaje 9,000 tun daga shekarar 2011 zuwa yanzu.
Source :naij hausa