Mun samu labari cewa akwai wasu tsirarrun ‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya da ke kokarin ganin ba a sauya tsarin zaben 2019 ba wanda wasu ke tunanin ana yunkurin yi ne domin kawowa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikas a zaben mai zuwa.
Tsohon Shugaban Sanatocin Arewa watau Abdullahi Adamu ya bayyana cewa akwai akalla Sanatoci 59 da ba su yi na’am da yunkurin da ake yi na canza tsarin gudanar da zabe ba. Sai dai Majalisar ta dage da ganin cewa ta maida zaben Shugaban kasa karshe.
Bayan shi tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa watau Sanata Abdullahi Adamu akwai kuma Sanaata Ali Wakil (Bauchi); da Abdullahi Gumel (Jigawa); Umar Kurfi (Katsina); da Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi) da duk ba su yarda a taba tsarin zaben na 2019 ba.Har wa yau akwai Sanata Garba Masi (Adamawa); da wasu Sanatocin Kudancin kasar irin Ovie Omo-Agege; Andrew Uchendu; da Benjamin Uwajimogu.
Wasu ma na ganin Majalisar ba ta da wannan hurumi kuma da dama ma ba su yi na’am da hakan ba.
Source :naij hausa
Title :
Yan Majalisan Dake Kokarin Kare Buhari A Majalisar Dattawa
Description : Mun samu labari cewa akwai wasu tsirarrun ‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya da ke kokarin ganin ba a sauya tsarin zaben 2019 ba wanda wasu ke...
Rating :
5