A ranar Juma'ar da ta gabata ne wata Kotun Birnin Ingolstadt ta kasar Jamus, ta zartar da hukuncin dauri na shekaru 9 da rabi kan wani manomi da laifin yunkuri na kashe iyayen sa da shinkafar bera.
Wannan Kotu dai ta la'anci wannan mutum mai shekaru 53 a duniya, inda ta kama shi da laifi dumu-dumu na yunkurin kisa.
A cewar Alkalan Kotun, wannan dattijo dai ya yi Odar shinkafar bera tun daga kasar Sin, kuma ya gauraya ta cikin abincin gyatuman sa tun a karshen shekarar 2016 da ta gabata.
Tarayyar jaridun Leadership da kuma The Punch sun ruwaito cewa, Likitoci na asibitin Jami'ar Regensburg sun nuna kwarewar aikin su, inda suka ceto rayuwar Mahaifin sa mai kimanin shekaru 81 da kuma Mahaifiyarsa mai shekaru 77 a duniya.
Sai dai wannan mutum ya shaidawa Kotun cewa, ko kadan bai nufaci kashe iyayen sa ba domin kuwa ya watsar da wannan shinkafa ta bera bayan ta karaso gareshi, inda ya zargi wata 'yar uwa ta sa da aikata wannan mugun nufi.
Source :naij hausa
Title :
Wani Matashi Ya Sa Wa Iyayensa Shinkafar Bera Don Su Ci Su Mutu
Description : A ranar Juma'ar da ta gabata ne wata Kotun Birnin Ingolstadt ta kasar Jamus, ta zartar da hukuncin dauri na shekaru 9 da rabi kan wani m...
Rating :
5