A sakamakon ci gaba da gudanar da atisayen dakarun sojin kasa mai taken Tseren Kyanwa, sun yi nasarar cafke wasu sakakkun shanu yayin da suke kiwo cikin gonakin mutane a kauyukan Yeas, Kaseyo da kuma Ukaa na karamar hukumar Awe ta jihar Nasarawa.
A yayin haka kuma, dakarun sun yi nasarar damkar wasu makiyaya tare da makamai yayin da suke kiwon shanu su wajen barnatar da amfanin gona da gangan na manoma.
Rundunar dai ta bayyana cewa, ta mika wannan 'yan ta'adda zuwa ga hukumar 'yan sanda domin ci gaba da hukuncin da ya dace.
Jaridar naij hausa ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin bincike kan Bukola Saraki da Ike Ekweremadu, dangane da yadda suka mallaki wasu manyan kadarori na makudan dukiya a birnin Landan.
Source :naij hausa