A ranar Litinin ne aka cika makwanni biyu cif-cif da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka sace 'yan mata dalibai 110 a makarantar sakandaren 'yan mata dake garin Dapchi a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.
Kawo yanzu dai babu duriyar yaran duk da ikirarin gwamnati ke yi na kokarin ceto su, yayin da iyaye da sauran 'yan uwan daliban ke ci gaba da zama cikin jimani.
Wasu 'yan bindiga ne dai suka kai hari a Dapchi, wanda ke da nisan kilomita 275k daga Chibok, a ranar 19 ga watan Fabrairu, lamarin da ya sa dalibai da malaman Makarantar Koyon Kimiyya da Fasaha ta mata suka ranta a na kare zuwa cikin dazukan da ke kusa.
Wannan lamari dai ya tuna wa duniya sacewar da 'yan Boko Haram suka yi wa 'yan matan makarantar sakandaren Chibok a shekarar 2014.
Iyayen yaran da aka sace sun nuna matukar rashin jin dadinsu a dai-dai lokacin da rahotanni ke cewa sojoji sun janye daga wuraren binciken ababen hawa da ke Dapchi wata guda kafin aukuwar lamarin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce satar yaran wani "babban bala'i ne" sannan ya nemi afuwar iyayen matan kan abin da ya faru.
Gwamnatin Najeriya dai ta ce, ta tura karin dakarun tsaro da jiragen yakin domin nemo 'yan mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ce ta sace su.
Satar dalibai 110 ta haifar da yanayi iri-iri ga rayuwar jama'ar garin da ma na wajen garin.
Kungiyar Boko Haram wacce ake zargi da kai hari a makarantar, ba ta ce komai ba kawo yanzu.
Source :bbc hausa