Sa'a ta karewa wasu mutane biyar bayan sun yi amfani da wani sindari mai fashewa domin fasa bututun danyen man fetur a jihar Bayelsa.
Majiyar jaridar Vanguard ta rawaito cewar mazauna wani kauye dake kusa da bututun ne su ka tsinci gawar mutanen ranar 25 ga watan Fabrairu, 2018, a surkukin Azagbene dake karamar hukumar Ekeremor.
Mutanen sun yi kokarin fasa bututun ne da sindarin "Dynamite" mai fashewa kamar yadda mutanen kusa da wurin su ka tabbatar da cewar sun ji karar fashewar sindarin da sanyin safiya kafin daga bisani su hangi tashin wuta na ci ganga-ganga.
Sai dai bayan mutanen kauyen sun isa wurin sai su ka iske gawar mutane biyu yayin da su ka samu ragowar mutane uku cikin mawuyacin hali.
Kakakin hukumar 'yan sanda jihar Bayelsa Mista Asinim Butswat ya ce ba a sanar da su afkuwar lamarin ba a hukumance.
Source :naij hausa
Title :
Sa'ar Wasu Barayin Mai Yaqare
Description : Sa'a ta karewa wasu mutane biyar bayan sun yi amfani da wani sindari mai fashewa domin fasa bututun danyen man fetur a jihar Bayelsa. M...
Rating :
5