Emanuella, ja'irar yarinya mai barkwanci a bidiyo, ta sake samun tagomashi, tun bayan da tasharta ta bidiyon youtube ta hada masu bibiya mutum miliyan guda, sai kara sama-sama take yi inda ta zama hamshakiyar mai kudi.
Yanzu dai shugaban Majalisar Dattijai, na ukku a kasar nan, ya gayyaceta majalisar a duk ranar da ta iso Najeriya domin su duba yadda zasu taimaka mata da ma sauran yara masu kwakwalwa kamarta.
A sakonsa ta tuwita, dattijoon ya taya ta murna da gayyatar da kamfanin fina-finan Hollywood wato Disney World, suka yi mata domin ta fara fitowa a fina-finansu.
Sarakin, bayan taya ta murna, ya kuma ce taje da ikon Allah, kuma yana mata fatan zata baiwa duniya dariya kamar yadda a shekarun nan take yi ga 'yan Najeriya.
Duniya dai na fara kallon kasar nan a matsayin kasa mai kima, da kwakwalwa, tun bayan da muka yi zarra a fannin tattalin arziki.
Source :naij hausa
Title :
Majalisar Dattawa Sunkira Emanuella Domin Su Taimaka Mata
Description : Emanuella, ja'irar yarinya mai barkwanci a bidiyo, ta sake samun tagomashi, tun bayan da tasharta ta bidiyon youtube ta hada masu bibiya...
Rating :
5