Daga Rariya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci daurin auren 'yar gwamnan jihar Kano kuma shi ne waliyin Amarya Fatima Umar Ganduje, inda Bola Ahmed Tinubu shi ne waliyin Ango Idris Abiola Ajimobi dan gwaman jihar Abia wanda aka daura a babban Masallacin Juma'a na jihar Kano.
Wanda Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, ya daura auren akan sadaki Naira dubu 50,000 kacal an kuma lakadan a bisa shaidawar dubban Al'ummar daga ciki da wajan jihar Kano.
Daurin Auren ya samu halartar shugaban majalissar dattawa Bukola Saraki, gwamnonin jihohi, ministoci, 'yan majalissun dattijai da na wakilai na tarayya, sarakuna da kuma hamshakan attajirai masu kudi wanda suka hada da babban dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Muhammad Indimi da kuma Alhaji Aminu Dantata da sauran manyan mutane 'yan uwa da abokan arziki.