Gwamnonin yankin Arewacin Najeriya sun yi taron ganawa da shuwagabannin kungiyar makiyayan Najeriya ta kasa, Miyetti Allah da nufin shawo kan matsalolin tsaro dake tsakaninsu da manoman Najeriya.
Daily Nigerian ta ruwaito wannan taro ya gudana ne a garin Sakkwato, inda ya samu halartar shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Kashim Shettima na jihar Borno, Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sakkwato, Nasir El-Rufai na Kaduna da kuma Abdullahi Ganduje na jihar Kano.
Majiyar jaridar naij ta ruwaito duk dayake basu fitar da bayanan bayan taro ba, amma rahotanni sun tabbatar da cewar gwamnonin tare da kungiyar sun tattauna game da tushen wannan rikice rikice tsakanin makiyaya da manoma da kuma hanyoyin magance matsalar.
A farin taron, gwamna Kashim ya bayyana cewar gwamnonin Arewa su 19 sun damu kwarai da gaske game da lamarin, sa’annan ya tabbatar da cewar zasu kawo karshen matsalar, ta hanyar goyon bayan dukkanin tsare tsaren da gwamnatin tarayya ta shirya game da hakan.
“Mun gaji da matsalolin tsaron dake faruwa a Arewa, muna ganin yadda matsalar Arewa maso gabas ke cikin mawuyacin hali, don haka zamu saurari dukkanin bangarori, don sanin sahihiyar hanyar magance matsalar” Inji Shettima.
Ta bangaren Miyetti Allah kuwa, shugabanta Muhammed Kirowa ya bayyana ma gwamnonin cewar matakan da wasu shuwagabannin siyasa ke dauka na magance rikicin bai dace ba, don haka ya shawarci gwamnoni da su dauki matakan da ba zasu cutar da wani bangare ba.
Dayake taron na jihar Sakkawato bai samar da wata takaimaimen hanyar magance matsalar ba, don haka ake sa ran cigaba da gudanar da irin taron a jihohin Filato, Abuja, Makurdi da Kaduna a nan gaba kadan.
Source :naij hausa