Usumanu dan Fodiyo, malami ne na addinin Islama, da yayi ta ggwagwarmayar kafa daular ISlama karkashin kalifofi da ke mulki a Santambul ta Turkiyya a yau.
Ya sha gwagwarmaya da sarakunan yankinsa, wadanda yace suna bin dagutu ne basu aiki da sharia.Ya rubuta littafai akalla dari, wasu da larabci, wasu da fillanci, inda ya sami almajirai da yawa wadanda suka zama mabiya kuma suka taya shi jihadi a arewacin Najeriya har ya cin garururwan Hausawa ya dora kabilarsa Fulani wadanda har yau su suke mulkar jama'ar yankin a sarautar gargajiya.
Garuruwa da yaci da yaki sun hada Gombe, Bauchi, Zazzau, Sokoto, Zamfara, Katsina, KAno da Adamawa.A yanzu dai jihadin ya fadi, tun bayan da turawa suka zo suka kwace daular suka kafa mulkin dimokuradiyya, suka kori wadanda suka ki karbar canji, wadanda a yanzu haka suna zama a can kasar Sudan a jihar Blue Nile.
Daga fara jihadin na Danfodio a 1804, zuwa sanda Turawa suka kori jikansa kalifa Attahiru, da malaminsa Modibbo Adama, da ma sauran baradansa, wadanda suka yi shahada Burmi ta Gombe a yau a 1903.
Usumanu dan Fodio dai, bai fara nasa jihadin ba, sai da ya shirya tsaff, ya tara almajirai, yya hada kansu, ya karantar dasu ilimin addinin Islama, ya koya musu ladubban jihadi da ma tsarin sharia, sannan ya sami mubayi'ar manyan malamai, da ma kuma 'sahalewar ubangijinsa'. (Jihadin Usmanu dan Fodio by Ibrahim Suleiman).
Dattijon, ya yaki sarakuna da yace suna hada mulkinsu da cuwa-cuwa, rashawa, tsafi, chamfi, murdiya, da ma kin bin taffarkin Islama, inda suka fi baiwa gargajiyar yankin karfi, maimakon tafida tsarin Islama.Sai dai shima Malamin, malaman tarihi sun zarge shi da kabilanci, inda dukkan wadanda ya baiwa tuta, suka fito daga tsatsonsa na Fulani, wadanda kuma suka dinga tsige sarakuna da suka gaji mulkin, wadanda asali su suka fito daga kasar da yankin, aka kore su arewa zuwa Nijar ta yanzu, wasunsu aka kashe, wasunsu kuma suka yi kudi zuwa cikin kasar Nupe da Yarabawa, (Hogben 1933: The Mohammedan Emirates of Nigeria).
Wadansu mayakan dai a zamanin nan, na kokarin sai sun dawo da daular, kamar yadda suke fadi, jihadin mujaddadi suke kokarin yi, amma dai ga alama jama'ar yankin sunyi hannun riga da jihadi a sun rungumi boko da dimokuradiyya, koda yake ana dan dana shari'ar a kaikaice a wasu jihohin yankin.
Source :naij hausa