Mun samu labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki tayi wa Jam’iyyar adawa ta PDP dukan babban-bargo a zaben kananan Hukumomin da aka yi a Jihar Edo. Jam’iyyar ta APC mai mulki a Jihar ta lashe zaben kananan Hukomi 7.
Yau aka cigaba da kirga kuri’un.
Jami’in zaben ya sanar da cewa Oteh Omoru ne yayi nasara a karamar Hukumar Akoko-Edo. A Karamar Hukumar Ovia kuwa, Destiny Enabulele ne yayi nasara da kuri’u 56,664.
A Makwabta Ovia ta Arewa maso gabas kuma Ogbemudia Osaze ne yayi nasara,A sauran kananan Hukumomin ma dai irin su Uhunwode, Egor, da Yammacin Owan, duk Jam’iyyar ta APC ce tayi nasara da kuri’un da su ka ribanya na sauran Jam’iyyun da su kayi takara irin su SDP.
Source :naij hausa
Title :
APC Tayiwa PDP Rubdugu A Edo
Description : Mun samu labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki tayi wa Jam’iyyar adawa ta PDP dukan babban-bargo a zaben kananan Hukumomin da aka yi a Jihar E...
Rating :
5