Mun samu labari cewa wani bangare na Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya cika alkawarin da su ka daukarwa ‘Yan Najeriya shekaru 3 da su ka wuce.
Shugaban Bangaren Jam’iyyar da ke Kasar Birtaniya watau APC UK Dr. Phillip Idaewor ya nemi Shugaban kasa Buhari ya tabbatar da cewa ya cika alkawuran da su ka dauka a lokacin yakin neman zaben shekarar 2015.
Dr. Idaewor ya ke tabbatar da cewa duk Najeriya babu Jam’iyyar da ta ke da shiri da muradun yin gyara irin APC inda ya kara da cewa Jam’iyyar ta dauki rai da daraja.
Shugaban Jam’iyyar a kasar Ingila ya kuma yi kira kan hadin kai.Phillip Idaewor ya yabawa Shugaban kasa Buhari na nada Asiwaju Bola Tinubu domin ya shawo kan barakar da ke cikin Jam’iyyar. APC UK tace dai manyan manufofin ta su ne aiki a kasa da yi wa Jama’ar Najeriya hidima tukuru.
Source :naij hausa
Title :
APC Ta Bukaci Buhari Ya Cika Alkawuran Da Suka Musu
Description : Mun samu labari cewa wani bangare na Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya cika alkawarin da...
Rating :
5