Mun samu labari na musamman daga Yerwa Express game da yadda ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka sace wata Baiwar Allah da ke aiki da Malaman asibiti a Garin Rann a karshen makon can.
A Ranar Alhamis ne ‘Yan Boko Haram su ka kai hari a Garin Rann cikin Karamar Hukumar Kala-Balge da ke Jihar Borno inda su ka kashe akalla mutum 8 su ka kuma sace mutum 1 wanda aka gano cewa wata Budurwa ce da ke aikin asibiti.
Wannan yarinya mai suna Hauwa Muhammad Liman tana aiki ne da wata Kungiyar bada agaji ta kasar waje na ‘dan lokaci. Wannan Budurwa dai ba ta fadawa mutanen gidan su inda ta ke aiki ba don kuwa jama’a sun dauka tana Garin Gomburu.
A lokacin da ‘Yan ta’addan su ka iso su na ta faman harbi, wannan Malamar asibiti ta aika sakon sauti zuwa wani ‘Dan uwan ta inda ta rika kukan cewa ga shi nan ana shirin tserewa da su. Shekarar wannan Yarinya 24 kuma ‘Daliba ce a Jami’ar Maiduguri.
Source :naij hausa
Title :
Abinda Budurwan Yan Boko Haram Tafada Kafin A Tafi Da Ita
Description : Mun samu labari na musamman daga Yerwa Express game da yadda ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka sace wata Baiwar Allah da ke aiki da Malaman asi...
Rating :
5