Kotun Tarayya ta daga sauraron karar tsohon mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro a kan zargin da ake masa da wawushe kudaden gwamnati, zuwa 2 da 3 ga watan Mayu, don cigaba da sauraron karar.
Alkalin Husseini Baba-Yusuf, ya bayyana sabon lokacin da aka sanya a birnin tarayya, bayan hukuncin da aka gabatar masa na kotun koli data yanke masa a ranar 2 ga watan Maris, 2018, wanda ta bada umurnin hanzarta shari’ar.Ya tabbatar da cewa za’ayi la’akari da zargin da ake yiwa Sambo Dasuki da wasu mutane, na laifukan biyu da ake zarginsa da aikatawa, kotun ta sanya 13 ga watan Afirilu a matsayin ranar shiryawa sauraron karar wanda manyan lauyoyi bakwai (SAN) na tarayya ne zasu halarta, don samun matsaya guda ta hanyar duba takardun masu kara da wandanda ke kare wanda ake tuhuma suka gabatar a shari’ar da aka fara tun 2015.
Manyan lauyoyin da zasu halarci taron sun hada da Rotimi Jacobs, mai kara, sai Ahmed Raji, Akin Olujimi, Olajide Ayodele, Kayode Olatoke, Hakeem Afolabi, da kuma Solomon Umoh wadanda suke tsayawa wadanda ake kara daban-daban sun yarda da hukuncin kotun koli na hanzarta shari’ar da kuma taron shiryawa shari’ar.
Inda Ahmed Raji, mai shugabantar lauyoyin masu kare Dasuki, ya fadawa kotu cewa da hukumar kula da tattalin arziki ta kasa da hukumar ‘Yan Sanda masu farin kaya manufarsu ta bambanta kuma ba gwamnati daya sukewa aiki ba.
Gwamnatin tarayya tana zargin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro Sambo Dasuki; tsohon Daraktan kudi Salisu Shu’aibu; shugaban kamfanin Acacia Holding Limited da Asibitin Reliance Aminu Baba-Kusa, bisa zargin dibar kudin gwamnati ba akan ka’ida ba da kuma zamba.
Wadanda ke a kotun lokacin shari’ar banda Dasuki sun hada da tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa; da tsohon Ministan kudi na jiha, Bashir Yuguda, duk sun gurfana don amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
Title :
A Hanzarta Yin Shari'ar Dasuki - Kotun Koli
Description : Kotun Tarayya ta daga sauraron karar tsohon mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro a kan zargin da ake masa da wawushe kudaden gwamn...
Rating :
5