Wannan dai abu ne da ba safai ake ganin an yi ba, matar mai shekara 49 'yar asalin kasar India, malamar makaranta ce da dan ta ya rasu ya na da shekara 27 bayan fama da cutar Kansa shekaru biyu da suka gabata.
Ta samu wata mace mai shekara 35, inda aka debi maniyyin dan na ta kafin a binne shi aka dasawa a mahaifar matar. Kuma Allah cikin ikonsa matar ta haifi 'yan biyu, aka radawa daya daga ciki sunan mahaifinsa.
Ta ce ta dauki matakin ne dan kar a manta da dan na ta baki daya, saboda ya rasu ko auren fari bai yi ba.
Bayan kammala digiri kan aikin injiniya a jami'ar Pune da ke kasar, matashi Prathamesh ya wuce kasar Jamus dan yin digiri na biyu a hekarar 2010.
A shekarar 2013 aka gano Prathamesh ya na dauke da cutar Kansar kwakwalwa, ya kuma mutu bayn shekara 3
A shekarar 2013, aka gano ya na fama da cutar Kansar kwakwalwa, kuma bayan shekara uku ya rasu. Ga bannin mutuwarsa ne aka samu diban maniyyinsa aka adana a sibiti daga bisani aka dasa a mahaifar wata mace ta kuma haifi 'yan biyu.
A lokacin da aka haifi 'yan biyun, mahaifiyarsa ta yi farin ciki inda ta kara da cewa ''Prathamesh di na ya sake dawowa,'' inji ta.
Ta kara da cewa '' Na yi matukar shakuwa da Da na. Yaro ne mai kaifin basira, tun da ya shiga makaranta na ke alfahari da shi.
Ya na karatun digiri na biyu ne ya kamu da wannan cuta a kasar Jamus, dan haka na dauki matakin gaggawa na adana maniyyinsa da nufin na samu jikokin da za su dinga tuna min da shi.''
Tun da fari daman likitoci sun bada shawarar ayi gaggawar dibar maniyyin matashin, kafin a fara masa maganin cutar Kansar.
Gabannin mutuwar Prathamesh, ya amince mahaifiyarsa da 'yar uwarsa mai suna Dnyanashree, su debi maniyyin sa dan amfani da shi ga wata macen.
'Yan biyun da aka haifa bayan mutuwar Prathamesh , inda aka sanyawa macen suna suna Preesha namijin kuma ya ci sunan mahaifinsa Prathamesh
A lokacin da Rajashree ta dauki matakin, ta na ganin kamar ba zai yiwu ba.
Shekaru biyu bayan mutuwar dan na ta, Rajashree ta ki yadda ta yi kukan mutuwarsa, saboda ta na ganin 'ya'yansa da suke tuna ma ta da shi. A ranar 12 ga watan Fabrairu 2018 aka haifi tagwayen masu cike da tarihi.
Dakta Supriya Puranik, da ta jagoranci aikin ta ce abu da ba a saba gani an yi ba
Bayan ta yanke shawarar yin dashen, suka daidaita da asibitin Jamus din. Suka aike da maniyyin dan na ta, babban asibitin Sahyadri da ke Pune wadanda suka jagoranci aikin.
Dakta Supriya Puranik, kwararriyar likita ce a asibitin ta ce ba ta taba ganin irin wannan kauna da ke tsakanin Uwa da Danta ba. Ta nuna farin ciki da suka yi nasara aikin, kuma uwar Dan na cike da farin ciki.
Source :bbc hausa
Title :
Yadda Akeyi Nasamu Jikoki da Maniyyin Dana Daya Mutu
Description : Wannan dai abu ne da ba safai ake ganin an yi ba, matar mai shekara 49 'yar asalin kasar India, malamar makaranta ce da dan ta ya rasu y...
Rating :
5