Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya kai wa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ziyara a gidansa da ke Otueke da ke kudu maso kudancin kasar.
Cif Obasanjo ya je jihar Bayelsa ne domin kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta yi, a cewar jam'iyyar PDP da ke hamayya a kasar.
"Daga nan ne ya kai ziyara wurin Goodluck Jonathan a gidansa da ke Otuoke," in ji PDP, a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Mr Jonathan da mai dakinsa Patience ne suka tarbi tsohon shugaban kasar.
A baya dai, Obasajo ya soki Mr Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulki a lokacin da yake shugabancin Najeriya, yana mai cewa Obasajo dai ya soki shugaba Goodluck Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulki, yana mai cewa Mr Jonathan na so ya sake cin zaben kasar ko ana so ko ba a so idan ba haka ba kuwa zai jefa kasar cikin rikici.
Buhari ya yi tsufa da sake tsayawa takara - Obasanjo
Obasanjo ya yi rijista da sabuwar kungiyarsa
Cif Obasanjo ya zama shugaban Najeriya sau biyu, kuma shi ne ya zabi shugaba Jonathan domin zama mataimakin marigayi shugaba Umaru 'Yar Adua.
A watan jiya, Cif Obasanjo ya soki Shugaba Buhari saboda "rashin iya shugabanci" inda ya yi kira a gare shi da kada ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar.
Ya kafa wata kungiyar siyasa da ya ce ita ce za ta iya ceto kasar daga kangin da take ciki.
Masu sharhi na gani tsohon shugaban gwano ne da ba ya jin warin jikinsa, suna masu cewa shi kansa bai iya mulki ba lokacin da ya yi shugabancin kasar.
Source :bbc hausa