A Ghana, kasar da aka kiyasta cewa tana da mutane sama da miliyan 28 a shekarar 2016, ba kowa ne ya san kwallon zari-ruga ba, ko da da sunan wasan na Ingilishi, wato Rugby.
Sai dai masu sha'awar wasan a karkashin jagorancin Hukumar Kwallon Zari-ruga ta Ghana sun dukufa don ganin labarin ya sauya.
"Tun baya da muka rungumi zari-ruga, sai [muka ga ya wajaba] mu kirkiri wani tsari…[wanda] a karkashinsa za mu bunkasa wasan a tsakanin matasa, da mata, kuma a fadin kasar nan", in ji Shugaban Hukumar, Herbert Mensah.
Wannan yunkuri da kuma burin da suke da shi na samar da 'yan wasa akalla 1,500 su suka aka daura damarar ganin an koyar da zari-ruga a makarantu 120 nan da shekarar 2020.
Wasan zari-ruga a makarantu
Hakan ne kuma ya kai ga horar da wasan a wata makarantar firamare ta Islamiyya mai suna Al-Walid da ke unguwar Kanda a birnin Accra.
Wakilinmu Muhammad Fahd Adam ya ziyarci makarantar inda ya tarar dalibai mata na atisaye, a filin wasa na makarantar mai jar kasa, galibinsu sanye da hijabi, wasu da takalmi wasu kuma babu ma takalmin a kafarsu.
Mai horar da su, Rafatu Inusa, ma'aikaciya ce a Hukumar Zari-Ruga ta Ghana ta kuma shaida wa BBC cewa: "Muna so a cikin unguwanninmu da makarantunmu kowa ya rungumi rugby, musamman yara mata saboda rugby wasa ne na kowa da kowa.
"Ba [wasa ne da za a ce mai] jiki ba za ta iya ta bugawa ba, ko [a ce] wata guntuwa ce; [ko] kana da jiki, [ko] ba ka da jiki, kowa na da [rawar da zai taka] a wasan rugby.
"A cikin yaran makarantun mun samu wadanda suke shiga kulob-kulob, don su samu damar buga wa tawagar kasa, don haka…mata duka muna son su rungumi wasan rugby".
A yanzu haka dai akwai kungiyoyin zari-ruga guda 13 a kasar ta Ghana.
Burin Hukumar Zari-Ruga
Burin Hukumar Kwallon Zari-Ruga ta Ghana shi ne samar da kwararrun 'yan wasa, musamman mata 'yan kasa da shekara 14, wadanda za su wakilci kasar a duniya.
Ga alama kuma sai sun dauki hanyar cimma wannan buri, don kuwa 'yan mata da dama a makarantar Alwalid tuni suka shiga buga wannan gasa ka'in da na'in.
A cewar Zainab Abdulrahman, "Na iya [wasan zari-ruga] sosai; ina so na zama kwararriyar 'yar wasan rugby".
Amma ba a nan burinta ya tsaya ba, tana kuma "so in gwada ma yayana da kannena".
"Wasa ne na maza?"
Wasu dai na ganin kwallon zari-ruga wasa ne na maza majiya karfi, musamman saboda yadda ake turereniya da sheka gudu da sauransu..
Amma wadannan 'yan mata da suka rungumi wasan sun ce ba haka lamarin yake ba.
A cewar Maimuna Muhammad Dawud, "Ni a ganina ba na maza ba ne [su kadai]; har da mata ma za su iya bugawa.
"Shi yasa nake sha'awarsa, kuma ina buga rugby [saboda] idan 'yan uwana mata suka gani, za su so su ma su buga."
To ko me ya sa aka zabi makarantar Islamiyya, kuma ta mata, don koyar da wannan wasa na zari-ruga?
Koci Rafatu, wadda ita ma Musulma ce, cewa ta yi wannan ba abin mamaki ba ne, "Saboda [duk da cewa] yaran musulmi [ne], kar ku duba wai addini kaza kaza…ke mace ki sanya hijabinki, ki tabbatar ko ina naki yana rufe, idan yana rufe babu abin da ba za ki iya yi ba.
"Tun da dai ba ku da maza za ku buga ba—mu mata zallanmu ne—ba [wata] mishkila".
Hukumar Kwallon Zari-Ruga dai ta ce zuwa yanzu a yunkurin tallata wannan wasa sai hamdala.
A cewar Mista Mensah, "Kamar kowanne shiri, za ka samu nasara ne idan akwai wadanda suka jajirce, kuma tabbas ni na jajirce.
A wannan shekara, a karo na farko, mun kaddamar da league na mata wanda aka samu nasarar kammalawa.
"An samu nasara a bangaren yawan kungiyoyin da suka fafata, an kuma yi nasara dangane da irin mutanen da suke buga wasan daga addinai daban-daban da kabilu daban-daban da sauransu.
"An samu gagarumar nasara saboda wasan ya yi armashi, an bi dokoki, an samu karancin raunuka, [kuma] akwai hamasa sosai, saboda haka abin ya burge matuka".
Source :bbc hausa