Isra'ila ta kaddamar da munanan hare-hare ta sama a wuraren da 'yan kungiyar Hamas ke zaune a zirin gaza, a matsayin martani game da harin bam da aka kai kan sojojinta.
Ta ce harin bam din ya raunata sojojinta su 4.
Rundunar sojin Isra;ila ta ce ta kai hari wurare 18 da 'yan kungiyar din suke zaune cikin har da waje da suke ajiye makamai da kuma hanyar karkashin kasa da ke kan iyaka da Isra'ila.
Kazalika wata tankar Isra'ilar ta bude wuta a wani waje da 'yan kungiyar Hamas din ke zaune.
Lamarin dai ya hallaka Falasdinawa biyu .
Sai dai sojojin Israilar sun ce mutanen na cikin wani gungun Falasdinu da suka doshi kan iyakar kasar kuma akwai alamar tambaya game da manufarsu.
Likitoci a Gaza sun ce an raunata Palasdinawa biyu, yayinda ba a ga wasu uku ba a hare haren da Israilar ta kai.
Source :BBC HAUSA