Da yamancin jiya Laraba ne wasu 'yan bindiga suka kai mummunan hari a kauyen Birani dake cikin karamar hukumar mulki ta Zurmi dake jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun bude wa motar 'yan kasuwan wuta ne, inda motar take dauke da mutanen kauyukan Birani, Tungar Fulani, Mayasa da Mashema, daga bisani kuma suka cinna wa motar wuta wadda take dauke da dimbin mutane inda hakan ya yi sanadiyar hasarar rayuka da jikkita mutane da dama.
Su dai 'yan bindigan sun tare wata hanya ne dake fita garin na Birani suka yi masu kwanton bauna inda suka tare wata motar 'yan kasuwa kirar (kanta). 'Yan kasuwan sun gama cin kasuwa ne kamar yadda suka saba duk mako a hanyar su ta zuwa garuruwansu sai 'yan bindigar suka bude wa motar wuta tare da kone dukkan mutanen dake ciki kuma suka cigaba da kashe mutanen da suka yi yunkurin kawo masu dauki.
Daga cikin muhimman mutanen da suka samu halartar sallar jana'izar akwai mai martaba sarkin Zamfaran Zurmi Alhaji Abubakar Atiku Muhammad, shugaban karamar hukumar mulki ta Zurmi Hon Dr Auwal Bawa Moriki, Hon Mannir Aliyu gidan Jaja, Hon Yusuf Moriki da dai sauran mutane da dama.
Title :
An Yi Jana'izar Mutane Sama Da 30 Da Wasu 'Yan Bindiga Suka Kashe A Karamar Hukumar Zurmi A Jihar Zamfara
Description : Da yamancin jiya Laraba ne wasu 'yan bindiga suka kai mummunan hari a kauyen Birani dake cikin karamar hukumar mulki ta Zurmi dake jiha...
Rating :
5