Sace dalibai 'yan mata sama da 100 daga makarantar kwana a arewa maso gabashin Najeriya na tattare da rudani.
Mun san cewa wasu gungun mayaka, da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun shiga garin Dapchi a jihar Yobe da yammacin Litinin, 19 ga Fabrairu.
Sun tunkari makarantar Sakandaren kimiya da fasaha ta mata, suna ficewa a hankali.
Da farko, an yi ikirarin cewa yawancin matan sun tsere kuma babu daya daga cikinsu da aka sace.
Amma daga baya kuma sai gashi hukumomi sun amsa cewa an sace 'yan Matan.
To shin wai menene ainihin abin da ke faruwa?
Me ya sa ba mu san me ya faru ba?
Tun da farko dai an fara shiga rudani ne daga wani malami, wanda ya zanta da manema labarai bayan an kai harin.
Ya ce mayakan suna neman abinci ne, ba sun je ba ne da niyyar garkuwa da wani. Ya kuma ce 'yan matan sun shuga daji ne domin buya.
Hakki ne ya kama gwamnatin Buhari — PDP
Jami'an tsaron Nigeria sun bazama neman 'yan matan Dapchi 110
Wasu na ganin kamar da farko gwamnati ta amince da bayanin malamin kafin daga baya ta yarda da cewa sace 'yan matan aka yi.
Amma duk da haka, rudanin ya kara yawa a labarin, a yayin da bayanai daga bangarorin gwamnati da sojoji suka yi ta karo da juna, har ta kai aka fito aka bayar da sanarwar ceto daliban, a dai dai lokacin da babu wani jami'in gwamnati ko na tsaro da ya fito ya sanar da cewa an sace su.
'Yan mata nawa aka sace?
Babban batun da ya fi jan hankali a rudanin labarin tsakanin iyayen 'yan matan da hukumomi shi ne yawan adadin daliban da aka sace.
Tun da farko iyayen sun dage cewa 'yan mata sama da 100 ne aka sace daga makarantarsu, da ke da yawan dalibai 926, yayin da kuma hukumomi suka ce adadin bai kai 50 ba.
Sannan hukumomin sun ci gaba da ikirarin cewa 'yan matan da dama sun gudu sun shiga daji, tare da cewa za su fito.
'Yan uwan daliban sun taru a makarantar Dapchi a yayin da suke jiran tsammani
Domin kawo karshen dambarwar, iyayen 'yan matan sun hada kansu inda suka fitar da jerin sunaye 105 na 'ya'yansu da aka sace.
Wannan ya sa gwamnati ta yi amai ta lashe, inda ta fito ta ce adadin 'yan matan da aka sace 110 ne.
Ko menene kamannin batun Dapchi da Chibok?
Editan BBC a Afirka Will Ross, ya lura da wasu abubuwa daga batun sace 'yan matan Chibok a watan Afrilun 2014 da ke kama da batun sace 'yan Mata a Dapchi.
Ya ce a lokacin, sojoji da gwamnati sun musanta labarin Chibok kuma ba tare da fitar da wani bayani ba a yayin da Boko Haram ta kwashi 'yan mata sama da 279 ta shiga daji da su.
A wannan karon ma an samu rudani, inda aka yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya kuma gwamnati ta fito ta nemi afuwa.
Bayan shekaru hudu da suka gabata, a yau kuma duniya ta sake cin karo da irin wannan al'amari na rudanin bayanai da kuma fushi daga iyaye.
Har yanzu akwai ragowar 'yan matan Chibok sama 100 da ake ci gaba da garkuwa da su.
Ko da ace hukumomi za su iya kubutar da su, amma har yanzu ba a ji duriyar 'yan matan Dapchi ba.
Me ya sa babu wani jami'in tsaro a Makarantar?
Duk da darasin da ya kamata ace an koya daga sace 'yan matan Chibok a 2014, amma kuma sai gashi yanzu ya kasance babu wani jami'in tsaro a makarantar Dapchi.
Kuma duk da haka iyaye na tura 'yayansu.
Wakilin BBC ya ce wannan na da nasaba ne daga fatan da mutane suke cike da shi bayan zaben shugaba Muhammadu Buhari a 2015, da kuma yadda sojoji suke ta nanata samun galabar yaki da 'yan Boko Haram.
Ya ce, sun san cewa akwai sojoji da shingayen bincikensu a kusa da garin, saboda gwamnan Yobe Ibrahim Gaidam ya shaidawa manema labarai cewa mayakan sun kai hari, sa'o'i bayan sojoji sun fice daga shingayen bincike a Dapchi.
Ko da yake rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin.
Me ya sa ba za su iya gano 'yan matan ba?
Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince cewa an sace 'yan matan, kuma daga karshe ta kaddamar da farautar gano su.
Shugaba Buhari ya ce rundunar soji da da jiragen sama za a yi amfani da su domin gano 'yan matan. Sai dai babu wani karin bayani game da binciken.
Wasu daga cikin Kayan daliban da aka sace a Dapchi
Sai dai kuma jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa tuni Mayakan Boko Haram suka fice da 'yan matan daga Najeirya zuwa makwabciyarta Nijar.
Amma idan har suna cikin Najeriya, wakilin BBC ya yi imanin cewa za a bi da su ne ta Dajin Sambisa, domin anan ne kawai za su iya boye wa saboda girman dajin.
A nan ne hedikwatar Boko Haram inda ta boye 'yan Chibok.
An yi ikirarin murkushe Boko Haram - Shin gaskiya ne
A watan Janairu ne Janar roger Nicholas kwamandan da ke jagorantar yaki da Boko Haram a arewa maso gabashi ya sanar da cewa an murkushe kungiyar Boko Haram.
Amma sace 'yan matan Dapchi ya nuna ba haka ba ne.
Source :bbc hausa