Shugaban Koriya ta Arewa ya ce shi fa ya na da makunnin nukiliya a kan teburinsa kuma zai bayar da umarnin amfani da makaman ne in har kasarsa ta fuskanci barazana.
A sakonsa na sabuwar shekara da aka watsa ta gidajen talbijin, Shugaba Kim Jong-un ya zolayi Amurka da kawayenta inda ya ce ba abu ne mai wahala yayi raga-raga da daukacin Amurka ba.
Sai dai ya ce kasar sa a shirye take ta tattauna da Koriya ta Kudu har ma ta tura tawagar 'yan wasa zuwa gasar Olympics a birnin .
Sai dai a lokacin da 'yan jarida suka nemi ya mayar da martani akan kalaman Kim Jong-un, shugaban Amurka Donald Trump ya ce, "zamu gani- zamu gani".
A kwanakin baya ne Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi mai tsauri.
Takunkumin zai kayyade ma Koriya ta Arewa ikon shigo da man fetur din zuwa ganga dubu 500 a shekara guda.
Hakan zai zaftare kusan kashi 90 a kudirin Kim Jong-un na son zama Shugaban kasar na har abada.
Fitar da man fetur din Pyongyang zai ragu da kusa kashi 90 cikin dari kuma za a bukaci 'yan Koriya ta arewar da ke aiki a wasu kasashen duniya da su dawo gida.
Kuma hakan zai dakile wata muhimmiyar kafa ta samun kudaden kasashen waje.
Source: BBC Hausa
Title :
Makunnin Nukiliya Nakan Teburina-Kim Jong Un
Description : Shugaban Koriya ta Arewa ya ce shi fa ya na da makunnin nukiliya a kan teburinsa kuma zai bayar da umarnin amfani da makaman ne in har kasar...
Rating :
5