Dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya doke dan wasan Barcelona Lionel Messi inda ya lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar duniya, wato Ballon D'Or karo na biyar - kuma karo na biyu a jere.
Yanzu dai dan wasan dan kasar Portugal mai shekara 32- ya yi kankankan da Messi, dan kasar Argentina mai shekara 30 wanda shekarar 2015 ce karon karshe da ya lashe gasar.
A kakar wasanni da ta wuce, Ronaldo ya taimaka wa Real Madrid wurin lashe gasar cin Kofin Zakarun Turai da kuma gasar cin Kofin La Liga da Real Madrid ta dauka, wanda a karon farko suka lashe tun daga shekarar 2012.
'Yan wasan biyu su suka samu kambin tara da aka bayar a baya a tsakaninsu, kuma daman ana kyautata zaton a wannan karon ma dan wasan na Real Madrid din ne zai karbe kambin ya zama yana da biyar daidai da na abokin hamayyar tasa Messi.
Dan Senegal da kungiyar Liverpool Sadio Mane da kuma takwaransa na Gabon da kungiyar Borussia Dortmund, Pierre Emerick Aubameyang su kadai ne 'yan wasan Afirka biyu daga cikin 30 da suka kasance cikin masu takarar ta bana.
George Weah, na Liberia wanda ya ci kambin a shekarar 1995, shi kadai ne dan Afirka da ya taba karbar kambin na Ballon D'Or tun lokacin da aka kirkiro da kyautar a shekarar 1962.
Source: BBC Hausa
Title :
Ronaldo Ya Doke Messi A Gasar Dan Kwallon Duniya
Description : Dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya doke dan wasan Barcelona Lionel Messi inda ya lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar duniy...
Rating :
5