Mahukunta a birnin Hyderabad da ke kudancin Indiya suna shirin bayar da tukwuicin rupee 500 ga duk wanda ya nuna maboyar mabarata.
Wannan wata dabara ce ta raba birnin da mabarata daga 15 ga watan Disamba.
Kwamishinanan 'yan sandan birnin ya kuma hana bara har na tsawon wata biyu.
Masu sukar lamarin sun ce wannan matakin ya biyo bayan wata ziyara da 'yar Shugaba Trump, Ivanka za ta kai yankin, amma mahukuntan sun musanta haka.
A makon da ya gabata dai an ga jami'an 'yan sanda na kama mabarata a wuraren ibada da tashoshin mota da na jirgin kasa.
Ana kai wadanda aka kama din zuwa wata cibiyar kula da marasa galihu da ke kusa da babban kurkukun birnin Hyderabad.
Ana sa ran Ivanka Trump za ta ziyarci Hyderabad domin ta halarci wani babban taro game da shugabanci a kasuwanci daga 28 zuwa 29 ga watan Nuwamba.
A watan Maris na 2000 ma an dauki irin wannan matakin a lokacin wata ziyara da Bill Clinton ya kai a lokacin yana shugaban Amurka.
M Sampat, wanda shi ne shugaban cibiyar ya fada wa BBC cewa: "Rupee 500 din wani tukwuici ne da kurkukun birnin yake bayarwa domin raba birnin Hyderabad da mabarata."
Ya kuma ce, "Kurkukun na fatan koya wa mabaratan sana'o'i domin su fara aiki a tasoshin sayar da mai da dama mu muke samar musu da ma'aikata."
Gwamnatin jihar ta ce ta kama mabarata 366 kawo yanzu. Daga cikinsu, 128 sun zabi suyi zamansu a cibiyar, inda 238 kuma suka koma gida, kuma sun yi alkawarin ba za su cigaba da bara ba.
Babban shugaban kurkukun Telangana, VK Singh ya fada wa BBC cewa: "Yawancin wadanda aka kama sun musanta cewa su mabarata ne bayan da aka kawo su nan."
"Mun rika sakin wasu daga cikin mabaratan bayan sun yi alkawarin cewa ba za su ci gaba da bara ba.
"Mu kan saka bayanansu a na'ura mai kwakwalwa domin mu iya gane su a gaba", in ji shi.
Jami'ai sun ce wannan matakin ya sa mabarata masu yawa daga cikin kimanin guda 5,000 dake cikin birnin sun yi kaura zuwa wasu biranen dake kusa.
Jam'an sun ce kalubalen da za su fuskanta shi ne na tabbatar da cewa mabaratan ba su koma birnin ba bayan 7 ga watan Janairun 2018, lokacin da hanin yin barar zai daina aiki.
Source:BBC Hausa
Title :
Zaa Bada Lada Ga Wadanda Suka Nuna Mafakar Mabarata
Description : Mahukunta a birnin Hyderabad da ke kudancin Indiya suna shirin bayar da tukwuicin rupee 500 ga duk wanda ya nuna maboyar mabarata. Wannan w...
Rating :
5