Majalisar Dinkin duniya ta ce mutane miliyan 60 ne suke fuskantar rashin bandaki a Nigeria.
Ta ce wasu sun mayar da gwata ko kuma leda wurin da zasu yi baya haya.
Sai dai wasu masana sun ce yin hakan na yin barazana ga rayukan mutane.
Shugaban wata kungiyar mai fafitukar samar da wadatattun bandakuna a Nigeria, Nature Uchenna Obiafo ya ce matsalar ce da ke haddasa cuttutuka sanadiyyar shan gurbattacen ruwa.
Sun kuma ce akwai wasu yankuna a birnin Abuja da aka yi wa bandaki guda a gidan da mutane arbain suke zama a ciki.
Nature Uchenna Obiafor ya yi kira ga hukumomi a kan su tashi tsaye wajan samar da wadadattun bandakuna.
A ranar 19 ga watan Nuwamba ta kowace shekara ce ake ranar bandaki ta Majalisar Dinkin Duniya.
Majalisar Dinkin duniya ta ce muhimancin ranar shi ne a fadakar aluma game da faidar samar da bandakuna a brane da kuma yankuan karkara.
Source: BBC Hausa
Title :
Mutum Miliyan 60 Ne Basuda Bandaki A Nijeriya
Description : Majalisar Dinkin duniya ta ce mutane miliyan 60 ne suke fuskantar rashin bandaki a Nigeria. Ta ce wasu sun mayar da gwata ko kuma leda wuri...
Rating :
5