Jami'an tsaro a Kamaru sun kashe mutum bakwai yayin da suke zanga-zangar neman ballewar yankin da ke magana da Turancin Inglishi, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Maganin garin Kumbo ya shaida wa BBC cewa mutum bakwai din da aka kashe a garinsa suke, ciki da fursunoni biyar wadanda aka kashe bayan an cimma wani gidan yari wuta.
Tun da farko dai jami'an tsaro sun yi arangama da masu zanga-zanga a yankin da ke amfani da Turancin Inglishi na kasar Kamaru.
Rahotanni sun ce jami'an tsaron sun rika watsa wa masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye don tarwatsa su.
Wadansu masu fafutika ne a yankin Bamenda da kuma Buea ne suka shirya zanga-zangar a ranar Lahadi.
Masu fafutikar sun yi zanga-zangar ne a ranar don sun dauke ta a matsayin ranar samun 'yancin kansu kuma don su bayyana wa duniya ,mawuyacin halin da yankin Kamaru mai amfani da Turancin Inglishi ke ciki.
Wakilin BBC Frederic Takang ya ce gobara ta tashi a wani gidan yari da ke garin Kumba a arewacin Bamenda.
Sai dai ba san abin da ya jawo hakan ba tukuna.
Al'amarin yana faruwa a daidai lokacin da hukumomi a kasar suka haramta zanga-zanga da kuma tarukan jama'a a yankin da ke amfani da Turancin Inglishi saboda tsoron kada su yi zanga-zangar neman ballewa.
A makon jiya ne gwamnatin kasar ta rufe iyakarta ta bangaren yankin da magana da Turancin Inglishi da Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Zanga-Zanga Ta Barke A kasan Kamaru
Description : Jami'an tsaro a Kamaru sun kashe mutum bakwai yayin da suke zanga-zangar neman ballewar yankin da ke magana da Turancin Inglishi, kamar ...
Rating :
5