A ranar Laraba ne jam'iyyar kwaminisanci ta China ta gudanar da babban taronta a birnin Beijing, karkashin jagorancin Shugaba Xi Jinping.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Chinar ke cika gaba da kulla kyakkyawar dangantaka ta fuskar kasuwanci da kasashen duniya, musamman nahiyar Afirka.
Najeriya na daga cikin kasashen da suka kulla alakar kasuwanci da gwamnatin Chinar, inda kasashen biyu suka fara ayyukan hadin gwiwa na ababen more rayuwa misali tashar Jirgin kasa ta zamani da aka bude a watan Yulin bara.
Tuni wasu matasa manoma 'yan Najeriya na cikin wadanda suka fara cin gajiyar kulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin su da wani kamfanin China.
Banagarorin biyu sun cimma matsaya a kan yadda za su rika gudanar da cinikin amfanin gona irin su citta da itacen katako a tsakaninsu.
Mahmud Nuhu Sulaiman shi ne wakilin kamfanonin China da suka zo Najeriya domin kulla dangantakar kasuwanci da 'yan kasuwar kasar, kuma ya bayyana wa BBC cewa kasar ta China ta riga ta kammala shirye-shiryen kulla dangantakar cinikayya da 'yan kasuwar Najeriya.
"Duk 'yan kasuwar da suke da kayan da China ke bukata za su kai kayansu wata ma'aikata ta musamman a nan Najeriya inda za mu duba kayan kuma mu biya 'yan kasuwar kai tsaye", in ji Mallam Mahmud.
Mahmud ya kuma bayyana cewa: "Akwai wani katako da ake kiransa Koso, wasu kuma na kiransa Madrid. To bayan mun sayi wannan katakon, sai mu sarrafa shi, wato mu tsaga shi kuma mu loda shi a cikin kontena. Daga nan sai mu tura kayan zuwa kasar Sin."
BBC ta tambayi Babaji Ibrahim, wakilin wata kungiya ta manoma, 'Bauchi Youth Farmers' alfanun da suke fatan samu daga wannan dangataka ta kasuwanci.
Ya ce "Wannan yarjejeniyar ta kunshi kayan gona iri biyu zuwa uku. Na farko ita ce citta, sai kwallon yazawa wato 'cashew nut' na ukun kuma shi ne katako".
Ya kara da cewa sun cimma wata matsaya dangane da cinikin katako, wanda har sun fara fitar da shi zuwa China.
"A bangaren citta kuma, mun kammala tattaunawa da su jiya, inda suka bayyana mana yadda tsarin kasuwancin yake a China", in ji shi.
Fauziyya Sa'idu Salisu wata 'yar kasuwa ce mai fitar da Citta zuwa kasashen ketare.
Ta ce, "Yan kasuwarmu za su sami karuwa mai yawa, saboda za mu rika sayen citta a lokacin da take kakarta sai mu adana ta har lokacin da farashinta ya tashi. Ka ga za mu sami alfanu mai yawa".
Amma ayar tambaya anan shi ne: Shin Wa yafi morewa da wannan shiri? Najeriya ko China?
Balarabe Shehu Ilela wani mazaunin kasar China ne, inda ya dade yana harkokin kasuwanci daga Najeriya zuwa China. Ya bayyana dalilin da yasa China ke neman kulla dangantakar cinikayya da nahiyar Afirka, musamman Najeriya:
"Idan kasa ta yi karfi wajen bangaren tattalin arziki, tana bukatar fadada harkokinta a siyasance domin ta taka rawa a tsakanin kasashen duniya.
A halin yanzu tattalin arzikin China ya bunkasa sosai har yana abin da masana ke kira 'over-heating' na kudaden zuba jari."
Ya bayyana cewa, "Wannan ne yasa dole take turo kamfanoninta na cikin gida da su fita waje, domin idan ta bar su a gida za a sami matsala", kuma tana son zama kasa mai karfin fada a ji, kamar Amurka".
Source: BBC Hausa
Title :
Wayafi Morar Wani Tsakanin Nigeria Da China
Description : A ranar Laraba ne jam'iyyar kwaminisanci ta China ta gudanar da babban taronta a birnin Beijing, karkashin jagorancin Shugaba Xi Jinping...
Rating :
5