A yawancin lokuta, matan da mazansu suka mutu na tagayyara kuma sukan fuskanci talauci. Wannan lamarin haka yake a Afirka inda mafi yawan irin wadannan matan basu da ilimin zamani da zai taimake su wajen lura da kansu ballantana yaransu. Amma duk da haka, wasu matan marasa ilimin zamani suna ayyukan da ba kasafai mata keyi ba domin kula da yaran nasu. Usman Minjibir na Sashen Hausa na BBC ya ziyarci wani wuri a Abuja babban birnin Najeriya inda wasu mata da mazansu suka mutu ke ayyukan fasa dutse domin biya wa 'ya'yansu kudin makaranta.
Patience Tanimu na cikin masu aikin fasa dutse a kauyen Gudaba dake kusa da birnin Abuja. Ta nade hannayenta kuma ta yi daurin dankwali da ake kira "ture ni kaga tsiya".
Ta kuke tana fasa dutse da wata katuwar guduma da ake amfani da ita wajen gine-gine, kuma tan zufa babu kakkautawa duk da yake tana karkashin wata lema.
Uwargida Tanimu na rera waka domin rage zafin aikin fasa dutsen da take yi.
"A gaskiya jikina ya kan yi min ciwo da dare. Amma na kan sha wasu kwayoyi domin in samu barci. Dole ne in zage damtse kamar namiji idan ina son yin wannan aikin".
Mijin Patience ya mutu a wani hatsarin mota kimanin shekara shida da suka gabata. Amma har yanzu tana tuna irin yadda waccan rayuwar ta kasance tare da maigidan nata.
"Tun mijina na da rai nake wannan aikin na fasa dutse. Ya so ya hana ni aikin kafin mutuwarsa, amma hakan bai yiwu ba".
Babban kalubale dake gaban wannan matar da 'ya'yanta shi ne na biya wa yaran kudin makaranta. Kuma gashi Patience bata da 'yan uwan da zasu taimaka mata.
"Bani da iyaye ko 'yan uwa. A halin yanzu nine komai ga yaran nan. Ni ke ciyar da su, na tufatar da su kuma nine ke ilmantar da su. Ina iya kokarina. Daya daga cikin 'ya'yana na son zama dan kasuwa. Wan kuma y ce yana son zama likita ne. Sauran yaran ma na da nasu burin".
Amma fasa dutse baya kawo isassun kudade duk da yake wannan sana'a ita ce take rike gidan na tsawon shekaru shida da suka gabata.
"Muna godiya ga Ubangiji. Duk da yake ana samu a sana'ar, amma ina fatar samun wacce ta fi wannan. Dalilin shi ne na kan fara aiki da karfe 6:00 na safe kuma in tashi da karfe 6:30 na yamma. Wasu lokutan na kan koma gida babu ko kwabo a hannu na. Amma wata rana kuma na kan samu abin da baya kasa fam biyar na Amurka".
A halin yanzu Patience na amfani da kudin da take samu domin biyan kudin makarantar 'ya'yanta. Ko lamarin zai dore sai Allah kadai ya sani. Wasu kuma na ganin kamata yayi masu hannu da shuni da ma gwamnati su taimaka wa iyalai irin na Patience, domin al'amarinta irin na sauran iyalai ne dake sassan Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Matar Dake Aikin Fasa Dutse Don Ciyar Da Kanta A Abuja
Description : A yawancin lokuta, matan da mazansu suka mutu na tagayyara kuma sukan fuskanci talauci. Wannan lamarin haka yake a Afirka inda mafi yawan ir...
Rating :
5