Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da daftarin kasafin kudin shekarar 2018 a wajen taron mako-mako na majalisar da aka yi ranar Alhamis a fadar shugaban kasa a Abuja.
Majalisar zartarwar ta ce nan ba da jimawa ba ne za a gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokoki ta kasar.
Ministan Ayyuka, Wutar Lantarki da Gidaje Babatunde Fashola, ya ce aikin shugaban kasar ne ya mika wa majalisar kasafin kudi kuma ya yi bayanin kan yadda za a kashe kudin.
Har ila yau ministan ya ce suna tattaunawa da bangaren majalisa don tsayar da ranar da shugaban kasar zai je ya mika mata daftarin kasafin kudin.
"A baya muna mika wa majalisar daftarin kasafin kudin ne a watan Disamba, amma a bana za mu ba su a wannan watan na Oktoba ne, akwai bambanci kan yadda aka saba gani," in ji shi.
Ministar Kudi Kemi Adeosun, ta ce an kashe naira biliyan 450 wadanda za a gudanar da ayyukan raya kasa da su a kasafin kudin shekarar 2017.
Bugu da kari, majalisar zartarwar ta karbi bukatar samar da wata sabuwar tashar samar da wutar lantarki a jihar Edo a zaman da ta yi na ranar Alhamis.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Kammala Kasafin Kudi Na 2018
Description : Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da daftarin kasafin kudin shekarar 2018 a wajen taron mako-mako na majalisar da aka yi ranar Alhamis ...
Rating :
5