Daruruwan mutane sun fantsama kan tituna don gudanar da wata zanga-zangar da ba a saba gani ba a Singapore.
Mutane na gudanar da wannan maci ne don nuna bijirewarsu ga zaben shugaban kasar wanda ba a yi takara ba a ranar Laraba.
An ayyana Shugaba Halimah Yacob a matsayin mace ta farko da za ta rike mulki Singapore.
Yayin zanga-zangar tsuke bakin an rika daga kyallaye da ke bayyana damuwa kan halin da dimokradiyya ta tsinci kanta a wannan kasa.
Ko da yake, ita shugabar nadi ce maimako wadda al'umma ta zaba.
Halima Yacob ta kasance 'yar takara maras abokin hamayya bayan an soke cancantar wasu.
Rashin cika ka'idar tsauraran dokokin shiga zabe na kasar, ya sa aka haramta wa 'yan takara hudu tsayawa a zaben.
Source: BBC Hausa
Title :
Zanga Zanga Ta Barke Kan Shugaban Kasan Da Baa Zaba Ba
Description : Daruruwan mutane sun fantsama kan tituna don gudanar da wata zanga-zangar da ba a saba gani ba a Singapore. Mutane na gudanar da wannan mac...
Rating :
5