Yankin Arewa-maso-gabacin kasar nan zai iya afkawa cikin sabon mummunan matsalar tsaro, matsawar gwamnatin tarayya ta kasa samar da wani kwakkwaran abin dogaro ga dubban matasa ‘yan bijilante, wadanda su ka sadaukar da rayukan su su na taimakawa wajen yaki da Boko Haram.
Wata kungiya mai zaman kan ta ce, mai suna International Crisis Group (ICG) ta yi wannan gargadin.
A cikin wani rahoto da ta fitar mai take: Matsalolin da Su Ka Zama Gaba Kura Baya Siyaki Wajen Yaki da Ta’addanci a Afrika, rahoton wanda su ka kafa hujja tare da yin bincike da nazari a kasashen Nijeriya, Uganda, Sudan ta Kudu da Saliyo, ya nuna cewa ‘yan yakin sa kai da aka sani da vijilante masu taimakawa a yaki da Boko Haram da sauran irin su a sauran kasashen, sun taimaka wa gwamnatocin kasashen su kwarai da gaske wajen samar da tsaro da kuma dakile hare-hare a yankunan su.
Nnadi Obasi, wanda shi ne babban mashawarcin wannan kungiya a kan harkokin vijilante, ya ce bijilante sun taimaka kwarai wajen kasancewar su wata gada ko matakala tsakanin farar hula da sojoji da sauran jami’an tsaro. Sun kuma agaza wa jihohi matuka wajen sake dawowa hayyacin su daga fatattakar da mahara su ka yi wa al’umma a baya.
Sai dai kuma rahoton ya yi kakkausan gargadi cewa Najeriya da sauran wadancan kasashe da aka lissafa ka iya afkawa cikin barazana, musamman idan ba a gaggauta kulawa da ‘yan bijilante ba, bayan cin nasara kan mahara da ‘yan ta’adda.
A Najeriya, wannan rahoton ya ce tsare-tsaren da gwamnati ta yi alkawarin samar wa wadannan matasa bai wanzar da wani abain a zo a gani ba.
Sai kungiyar ta sake yin gargadin cewa muddin wadannan alkawurra ba su tabbata ba, “Nijeriya na iya fuskantar sabuwar barazana daga wadannan hasalallun matasa a Arewa-maso-gabas. Wasun su ka iya afkawa cikin halin kwace, safarar miyagun kwayoyi da sauran ayyukan laifuka irin na rikakkun masu laifi.”
Rahoton ya kuma ja kunne cewa a yanzu fa wasu ‘yan bijilante na yi wa wasu ‘yan siyasa aiki, wadanda aka san su wajen yin kaurin suna su na daukar ‘yan daba sojojin-hayar su.
“Yayin da barazanar Boko Haram ke kara raguwa, to barankankamar ‘yan siyasa wajen amfani da ‘yan bijilante ka iya zama wata sabuwar barazana a yankin.”
Daga nan sai rahoton ya shawarci gwamnati da ta shata wasu manufofi, kudirori ko ajanda wacce za ta bada kulawa, sa’ido da kuma tallafawa ga wadannan matasan, tare kuma da sake dora su a kan hanyar rayuwa irin ta game-garin farar hula.
Irin wannan kulawa da za a ba su, za ta hada har da samar musu aiki a kananan masana’antu, tallafa musu su gina kan su da kuma daukar su aiki a matsayin masu gadi a ma’aikatu, cibiyoyi ko masana’antu masu zaman kansu..
Source: Premium Hausa
Title :
Za'a Fuskanci Barazana In Akayi Watsi Da Bijilante A Arewa Maso Gabas
Description : Yankin Arewa-maso-gabacin kasar nan zai iya afkawa cikin sabon mummunan matsalar tsaro, matsawar gwamnatin tarayya ta kasa samar da wani kw...
Rating :
5