Wata yarinya 'yar shekara 13 da ta mutu sakamakon cutar kumburin jijiyar kwakwalwa ta taimaka wajen ba da gudunmawar sassan jikinta ga mutum takwas, adadi mai yawa a tarihi.
Jemima Layzell, daga yankin Somerset a London, wadda ta rasu a 2012, ta ba da gudunmawar zuciya da tumburkuma da huhu da kodoji da karamin hanji da hanta ga yaro biyar.
Iyayen Jemima sun ce marigayiyar na da basira da tausayi kuma Allah ya ba ta fikira - don haka suna "matukar alfahari da wannan abin tarihi".
Hukumomin lafiya sun ce babu wani mutum da ya taba bayar da gudunmawa ga mutane da yawa kamar Jemima.
Matashiyar ta yanke jiki ta fadi ne ana shirye-shiryen bikin zagayowar ranar haihuwar babarta karo na 38, kuma bayan kwana hudu ta ce ga garinku nan a asibitin yara na Bristol Royal.
An yi wa mutum uku dashen zuciya da 'yan hanji da tumburkumarta a lokacin guda kuma mutum biyu suka samu kodojinta.
An raba hantarta inda aka dasa wa mutum biyu, sannan kuma wani maras lafiya ya samu gudunmawar huhunan da ta bari.
Akasari dai, ba a cika samun irin wannan gudunmawa ga adadin mutane masu yawa haka ba.
'Ta musammam ce kuma ba irinta'
Mahaifiyar Jemima, Sophy Layzell, mai shekara 43, kuma mai koyar da wasannin kwaikwayo da mahaifinta Harvey Layzell, dan shekara 49, kuma manajan darakta a wani kamfanin gine-gine, sun ce sun san Jemima na son ta ba da gudunmawar sassan jikinta.
Saboda sun yi magana a kan haka kwanaki kalilan kafin mutuwarta, bayan wani mutum da suka sani ya yi hatsari ya mutu.
Sophy ta ce Jemima ba ta taba jin batun bayar da gudunmawar sashen jiki ba kafin wannan lokaci, kuma ta yi ta dar-dar, amma dai ta fahimci muhimmanci abin."
Ta ce har yanzu suna jin bayar da gudunmawar sassan jikin 'yarsu, shawara ce mai wahala amma dai ita ce daki
"Duk iyaye na son 'ya'yansu su zama na musammam, kuma su kasance ababen alfahari.
"Jim kadan bayan mutuwar Jemima, mun kalli wani shiri dangane da yaran da ke jiran a yi musu dashen wani sashe na jiki," in ji Sophy.
A cewarta idan muka ce a'a, tamkar mun hana wa sauran mutum takwas damar rayuwa.
"Duk iyaye suna iya cewa a'a, don kuwa Allah ya yi mu ne mu kare 'ya'yanmu. Kawai dai mun kwan da sanin cewa Jemima ta amince a yi hakan shi ya sa muka ce eh.
'Da dama suna cewa a'a'
Cibiyar kula da ayyuka dashe da karin jiki ta shirin inshorar lafiya a Ingila ta ce daruruwan mutane ne har yanzu ke mutuwa ba gaira ba dalili a lokacin da suke jiran a yi musu dashe, son kuwa iyaye da dama suna kin ba da gudunmawa.
A bara, mutum 457 ne suka mutu lokacin da suke jiran samun dashe a cikinsu 14 kananan yara ne.
A yanzu haka akwai mutum 6,414 da ke cikin jerin wadanda ke jiran samun gudunmawa kuma sun hada da yara 176.
A shekara ta 2015, wani matashi da ya mutu Tom Wilson mai shekara 22 sakamakon tsurewar da ya yi bayan sandar kwallon hockey ta same shi a ka.
Ana jin gudunmawar sassan jikinsa da ya bayar, ciki har da fata da kashi da bargo ta taimaka wa rayuwar kimanin mutum 50.
Source: BBC Hausa
Title :
Yarinyar Data Kyautar Da Sassan Jikinta
Description : Wata yarinya 'yar shekara 13 da ta mutu sakamakon cutar kumburin jijiyar kwakwalwa ta taimaka wajen ba da gudunmawar sassan jikinta ga m...
Rating :
5