Fitaccen dan wasan barkwanci na fina-finan Hausa Sulaiman Yahaya, wanda aka fi sani da Bosho ya ce tsundumar da ya yi cikin harkar fim ce ta hana shi zama farfesa.
"Na samo sunan Bosho ne saboda lokacin da nake makarantar sakandare ina yawaita karatu.
Na kan kwashe kwana 15 ban yi cikakken bacci ba saboda yawan karatu.
"Shiga ta harkar fina-finai ce ta hana ni zama farfesa," in ji Bosho, a hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa.
Dan wasan ya ce sha'awarsa wajen karatu ce ta sanya yake amfani da wasu kalmomi na boko a fina-finansa.
"Za ka ji ina yawaita cewa 'A shekarar 1778 da na je Ingila sarauniya ta bukaci a dafa min shayi amma na ce tuwo nake so' ko kuma na cewa 'wane ne ubanka a Northern Nigeria', in ji Sulaiman Yahaya.
Bosho, wanda ya kwashe fiye da shekara 30 yana fitowa a fina-finan Hausa, ya kara da cewa ya rungumi bangaren barkwanci ne saboda shi dama mutum ne mai yawan son raha.
A cewar Bosho, "Na soma fim tun lokacin da ake wasan kwaikwayo na dandali; ni mutum ne mai son bunkasa al'adun Hausa da addinin Musulinci, shi ya sa na zabi zama dan wasan kwaiwayo.
"Na dauki al'adarmu da matukar muhimmanci kuma na soma fim ne tun lokacin da ake yin wasannin kwaikwayo a Gidan Dan Hausa da ke birnin Kano. 'Yan wasa irin su Danhaki da Mallam Mamman su ne gwanayena".
Dan wasan na Hausa ya nuna bakin cikinsa kan yadda masu shirya fina-finan Kannywood ba sa mayar da hankali wurin bunkasa al'adar Hausa, yana mai cewa, "hakan ne ya zubar da mutuncinmu a idanun masu kallo".
Ya kara da cewa saboda irin mummunan kallon da ake yi wa 'yan fim ya bude kamfanin hada fim wanda zai mayar da hankali wurin tallata al'adun Hausa.
Bosho ya ce akwai dangantaka mai kyau tsakaninsa da marigayi Rabilu Musa Dan Ibro.
"Ibro ya kan taso daga garinsu Danlassan ya zo nan [cikin birnin Kano] mu sha hira; shi mutum ne mai kokarin zumunci.
"Ni ma na kan je garinsu na sada zumunci kuma har yanzu ina ci gaba da zuwa mu gaisa da iyaye da iyalansa. Kafin ya rasu mu kan bai wa juna shawara kan al'amuran rayuwa. Allah ya jikansa", a cewar Sulaiman Yahaya.
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Film Na Zubar Mana Da Mutunci-Bosho
Description : Fitaccen dan wasan barkwanci na fina-finan Hausa Sulaiman Yahaya, wanda aka fi sani da Bosho ya ce tsundumar da ya yi cikin harkar fim ce ta...
Rating :
5