Rahotanni daga garin Banki da ke kudu maso gabashin jihar Borno, a kan iyakar Najeriya da Kamaru, na cewa wasu mayakan Boko Haram sun hallaka mutane 18 a daren jiya Juma’a.
A ‘yan watannin baya-bayannan dai ana fuskantar karuwar hare-haren mayakan na Boko Haram a Jihar Borno, inda zuwa yanzu akalumma suka nuna cewa daga ranar 1 ga watan Yuni, zuwa Alhamis din data gabata, akalla mutane 172 ne suka rasa rayukansu, sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya rawaito.
Sabon harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Sakataren hakokin wajen Birtaniya Boris Johnson, yace yanzu haka kasarsa na horar da sojojin Najeriya dubu 28,000 domin tinkarar mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, in da matsalar ta fi kamari.
Source: RFI Hausa
Title :
Yan Boko Haram Sun Halaka Mutane A Banki
Description : Rahotanni daga garin Banki da ke kudu maso gabashin jihar Borno, a kan iyakar Najeriya da Kamaru, na cewa wasu mayakan Boko Haram sun hallak...
Rating :
5