Da zarar an ambaci wayar salula abin da ke fara zuwa zukatan mutane shi ne, wata na'urar zamani mai saukaka isar da sako.
Ko dai ta hanyar sakon kar ta kwana, ko kiran gaggawa a fadi wani abu da a baya sai an dauki tsawon kwanaki kafin sakon ya isa inda ake bukata.
Wasu kuma za su iya kallon wayar salula a matsayin jakadiyar sada zumunci, ko ma 'yar aiken da isarta da wuri ka iya ceto rayuwar wani ko wasu mutane daga fadawa wani ibtila'i. Misali gobara, hadarin mota, rashin lafiya, kwantar da tarzoma, isar da sakon farin ciki ko akasin haka.
A takaice wayar salula na taka muhimmiyar rawa a rayuwarmu ta yau da kullum.
To amma kun taba zama kun baje kolin irin rawar da ta kan taka wajen haddasa fitina ko gurbata tarbiyya, da haddasa rashin jituwa tsakanin miji da mata ko abokan juna ko kawaye har ma da gurbata tarbiyyar 'ya'yanmu?
Badriyya Tijjani Kalarawi ta yi ma na nazari kan wannan batu
Lamarin ya samo asali ne da yammacin ranar 13 ga watan Agustan 2017, da misalin karfe 8 na dare, a lokacin ina zaune bayan gama cin abincin dare.
Ga al'adata na kan kalli labarai na tashoshinmu na gida da kuma waje, kana sai na kalli wasannin kwaikwayo na kasar Indiya da ake fassarawa da harshen Turanci.
Wayata na ji tana kira, da na duba sai na ga ashe wata abokiyar wasata ce da ba zan ambaci sunanta ba, bayan gaisawa ta bukaci don Allah na zo gidanta akwai abin da take son mu tattauna akai.
Ban yi kasa a gwiwa ba na tafi, abin da ya daga min hankali yadda na gan su cirko-cirko kamar an yi mutuwa, tambayar farko da na yi mata ba ta amsa min ba ta dai miko min wayar salular 'yarta samfurinIphone 7+.
Manhajar WhatsApp ce a bude, inda na ga wani suna 'Stranger' wato bako, na ci gaba da duba sakonnin da yake turowa 'yarta mai shekara 16 wadda a bana ta kammala karatun sakandare.
Sakonnin ba masu dadi ba ne, a takaice sakwannin badala ne hadi da hotunan tsiraicin maza da mata wanda mai wannan lambar yake aikowa matashiyar yarinya.
Bayanin da mahaifiyarta ta yi min shi ne kusan shekara uku da mahaifin yarinyar ya siya mata wayar salula, ta nuna kin amincewa da hakan amma ya yi biris da ita.
Kuma duk shekara sai ya sauya mata waya.
Wannan mutumin da aka sakaya sunansa da Stranger, sun hadu ne a irin kungiyar nan ta abokai da ake haduwa don sada zumunta da raha wato WhatsApp Group.
Ya dade yana mata dadin baki tun ba ta tura masa hotunan tsiraicinta har ta fara.
A takaice dai sai da muka lalubo lambarsa muka dangana da zuwa wajen hukuma, aka kira shi don a yi musu tsakani.
Abin takaicin garjejen kato ne da ya girmeta da a kalla shekara 10, dole mahaifiyarta ta karbe wayar salular da ta zama jakadiyar batawa 'yarta tarbiyya.
Ko kun san?
Wannan ke nan da aka san abin da ya faru, akwai iyaye da dama da ba su san abin da 'ya'yansu ke yi da wayoyin salula ba, kawayen da a baya kan zo gida don sada zumunta zamani ya kawo lokacin da ba sai sun zo gida ba.
Ta wayar salula ake tattauna ko wacce irin magana, don haka ba ko wacce uwa ce ta san adadin kawayen 'ya'yanta ko 'yarta ba.
Iyaye ba su damu da bibiyar halin da 'ya'yansu ke ciki ba, ko da kuwa a cikin gida ne bare kuma idan suka fita.
Iyaye kan dauka 'ya'ya sun yi bacci da dare, alhalin a wasu lokutan suna can yin wayar dare da ba a cajin kudi wato Free Call ko dai da kawaye ko kuma da samari.
Kuma a yawancin lokutan wayar da ake yi da tsakar dare, ta sha bamban da wadda ake yi da rana ido na ganin ido, daidaikun samari da 'yan mata ne ke tattaunawa kan wani muhimmin batu a irin wannan lokacin.
Yawancin iyaye mata da na tattauna da su kan batun rawar da wayar salula ke takawa a rayuwar 'ya'yansu musamman mata, labarin ba mai dadi ba ne, kamar dai yadda wata uwa da ta bukaci na sakaya sunanta ta shaida min.
''Zan iya fada miki daya daga cikin abin da nake yin da-na-sanin yi a rayuwata, shi ne bai wa Zainab (ba sunanta na asali ba) wayar salula a lokacin da ta fara makarantar sakandare.
"Abin da Babanta ya shaida min ya kuma ba ni kwarin gwiwa akai shi ne yana da muhimmanci a san duk lokacin da ta fita ko dai makaranta ko gidan biki da sauransu.
"Ban dai saki jiki ba gaskiya, amma daga baya na bar damuwar, wallahi in takaice miki batu wayar salula ita ta koyawa 'yata abubuwa guda uku;"
Ta lissafa su kamar haka:
Na farko Zainab ta daina karatu da dare sai dai waya da chatting da kawaye a cewarta.
Ta ci gaba da cewa yarinyar ta daina ayyukan gida da 'ya'ya mata ke yi wa iyayensu, sam ba ta son zama cikin 'yan uwanta don yin hira ko taya su aikin gida da ake ba su daga makaranta.
"Abu mafi ciwo shi ne, ta dalilin wayar salula Zainab ta rasa 'yancinta na diya mace, don kuwa ta hadu da wani shaidanin saurayi da ya yaudare ta da abubuwan kyale-kyale da take boyewa ba mu san da su ba da dadin baki."
"Ya gayyace ta liyafar na abokinsa, ta min karya da walimar murnar zagayowar ranar haihuwar kawarta za a yi ta shirya da kawar suka je a can aka sanya mata abin gusar da hankali a lemo.
"Daga nan sai mai aikuwar ta auku, wannan shi ne abin da ba zan taba mantawa da shi da wayar salula ta haddasa min ba.
"Na kuma san har na mutu ba zan manta da wannan abin takaici ba,'' in ji wannan baiwar Allah.
Wata uwar ta daban ta shaida min cewa, ''Ta wayar salula ita ma 'yarta ta hadu da kawaye bata gari da suka rinjaye ta, suka koya mata yawo.
"Ta kai ma ba ta zuwa makarantar Islamiyya, idan ta fita daga gida sai ta hadu da kawayen su tafi yawo.
"A can ta koyo shaye-shayen nan na zamani da ake ta fama da su, ba mu farga da rashin zuwanta Islamiyya ba sai da malaminsu ya aiko cewa ba ta cika zuwa makaranta ba, don haka yana son ganin mahaifinta.
"A lokacin da ya je ne muka san halin da ake ciki, amma sai ta yi mirsisi wai tana zuwa hadda ce da ba ta bayarwa shi ne dalilin da ya sa malamin ba ya ganinta.
"To a hankali kuma sai na lura tana yawan bacci, alhalin a baya ba ta cika baccin rana ba, sannan ba ta son kannenta su shigar mata daki.
"Sannan tana yawan shan lemon kwalba, kuma ba ta taba bari kannen su sha.
"Abin ya ishe ni na dage da sanya ido a kanta, ba a je ko ina ba na kama kwalaben Benilin da Emzoline a durowar gefen gadon dakinta.
"A halin da ake ciki baban ya hanata zuwa makaranta daga boko har islamiyyar, kuma ya sha alwashin aure zai mata kowa ya huta daman dan kanina yana mutuwar sonta, amma ta ki maida hankali.
"Kin ji yadda wayar salula ta janyo min salalar tsiya.''
Ire-iren wadannan labarai suna da tarin yawa, sai dai kuma ba duka aka zama daya ba.
Akwai yara 'yan mata da samari da yawa da suke amfani da wayar salula kuma babu abin da ya faru sai alheri, yana da kyau dai iyaye su mayar da hankali da sanya ido kan tarbiyyar 'ya'yansu.
Ina mafita?
Na tattauna da Muhammad Salihu Abubakar, wanda aka fi sani da Baban Sadik, wanda masani ne kan harkokin intanet, inda ya ce, yana da matukar muhimmanci iyaye musamman mata, su dauki matakin janyo 'ya'yansu a jiki, ba su kulawa da cikakken 'yancin shaida musu duk abin da ke damunsu.
"Bin kwakkwafin son sanin kawayen 'ya'yanmu ba lallai sai mata ba har da mazan, sanin daga gidan da wadannan yara suka fito.
"Kokarin nusar da 'ya'yanmu illar da ke cikin badala, da zantukan batsa da kallon hotunan tsiraici, ko kallon bidiyon da ake yin badala.
"Nusar da su muhimmancin amfani da lokaci wajen cimma wani buri na rayuwa, da zai amfane su da al'uma baki daya, misali neman ilimi.
"Lokaci zuwa lokaci karbi wayar salular daga hannunsu, ajiye ta a kunne ba ma tare da binciken komai a ciki ba.
"Da yin kokarin amsa duk kiran da ya shigo wayar don sanin wadanda ke yawan kira ko ake kiran.
Source: BBC Hausa