Gwamnatin jihar Lagos da ke Najeriya ta ce tana samun karin rahotannin da ke nuna mata na lakadawa mazajensu duka a jihar.
Kwamishinan shari'a na jihar Mr Adeneji Kazeem ya ce sun samu rahotanni da dama daga wurin mazajen da ke shan dan banzan duka daga wurin matansu, yana mai bayyana lamarin da cewa ya yi muni.
Ita ma shugabar hukumar yaki da cin zarafin mutane ta jihar, Misis Lola Adeniyi, ta shaida wa BBC cewa, "Ma'aurata maza 55 sun kawo karar matansu inda suke zargin sanya su cikin halin damuwa da furta bakaken maganganu da kuma lakada musu duka".
"Akwai uku da suka ce matansu sun yi musu dukan kawo-wuka, biyu daga cikinsu sun ce suna da shaida hotuna da ke nuna hakan; da yawa daga cikinsu suna so hukuma ta warware matsalolin ba tare da an kai kararsu a gaban kotu ba. Wasu mazajen kuma suna so ne a kai su asibit domin yi musu magani", in ji shugabar
Ba kasafai dai ake samun labarin kan yadda mata ke dukan maza ba.
Sai dai wata mata ta shaida wa BBC cewa tura ce ta kai bango shi ya sa muke yin raddi.
Ta kara da cewa, "Babu mamaki cin zarafin da maza ke yi wa mata a gida ne ya yi yawa shi ya sa matan su ma suke lakadawa mazajensu nasu duka. Ka san idan tura ta kai bango ba ka da mafita idan baka tashi ka kare kanka ba".
Source: BBC Hausa
Title :
Yadda Mata Ke Daka Mazajensu A Legas
Description : Gwamnatin jihar Lagos da ke Najeriya ta ce tana samun karin rahotannin da ke nuna mata na lakadawa mazajensu duka a jihar. Kwamishinan shar...
Rating :
5