Batun ma'aikata 'yan cirani da ke aiki a kasashen Larabawa, ya dade ana cece-kuce akai, da kuma yadda ake kai su yin ayyukan, wanda hakan wani bangare ne na cin zarafinsu don ana rarraba su gidajen aiki ne ta hanyar sadarwar intanet.
Wakiliyar BBC ta gano shafukan sirri na Facebook da suke amfani da su wajen kaucewa sa idon hukumomi.
A baya-bayan nan ne aka gano wasu sakonni a shafukan Facebook da suka yi dai-dai da masu irin wannan aikin.
"Ina neman mace mai aiki wacce ta zo da bizar ziyara ko yawan bude ido da za ta yi aiki a matsayin 'yar aikin gida."
"Ina bukatar mace mai aiki cikin gaggawa koda na wata daya ne ko biyu ko uku, har zuwa lokacin da zan yi tafiya a watan Disamba".
"Ina neman mai aikin da zata zauna 'yar Indiya ko Philippino da zata kularmin da jaririna dan wata biyu".
Kodayake shugabannin shafin sun gargadi 'yan kungiyar da kada su suke su karya doka, sakonnin wata hanya ce da ake cin kasuwar wacce ta haifar da intanet din sakamakon bincikin da aka yi da kuma kararrakin da aka shigar a Saudiyya.
A kasar Saudiyya da kuma wasu kasashen Larabawa da dama, ma'aikatan da suka zo daga Asia da kasashen Afirka na iya samun biza a karkakashin wani tsari da aka sani da "kafala".
Wani tsari ne da yake kula da baki wadanda suke zuwa aikin gida su zauna tare da wadanda suke wa aiki har tsawon lokacin da za su zauna.
Yawanci ana gudanar da tsare-tsaren aikin ne ta hanyar hukumar daukar ma'aikata a hukumance, sai dai cin kasuwar da aka fara yi a shafin intanet ta ba wa wasu ma'aikata da masu daukar su damar kaucewa tsarin.
Wata mai kare hakkin 'yan ci-rani Vani Saraswathi ta ce, "Babban dalilin da ya sa ake neman ma'aikatan a shafin intanet yana jan hankalin ma'aikatan, kuma daukarsu ta hanyar hukumar na da matukar tsada"
"Idan kuma za a yi maka aikin kwangila za ka biya ne daga kan fam 2,000 zuwa 4,000.... amma idan ka biyo ta shafikan intanet ba za ka biya ko sisi ba.
Da farko dai masu daukar 'yan aikin suna amfana, wata mai fafutuka a kasar Saudiyya ta shaida wa BBC cewa, suna samun ninki biyu na albashin masu aikin idan suka samu masu daukar ma'aikatan a shafin intanet wanda ya saba wa ka'ida.
Kasuwar ma'aikatan ta intanet ba ruwanta da makudan kudin da ake biya a hukumar, suna iya samun aikinsu kuma mai albashi da tsoka.
"Abin takaici shafikan intanet sun mayar da samun aikin abu mai wahala ", in ji Nawal Al Hausawi.
Ta ce kwanan nan ta samu hayar mai aiki bisa amincewar hukuma.
Akwai gomman kungiyoyin shafukan Facebook da suke dauke da dubban mambobi da suke saka mata neman aiki a matsayin masu aikin gida, kodayake ba dukkansu ba ne suke aiki ba bisa ka'ida ba.
Kuma shi kanshi tsarin kafala ya samu ne a karkashin kakkausar sukar da ake yi a kan cin zarafin ma'aikatan da kuma sauran ce-ce ku-ce.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta ce tsarin na ba wa ma'aikatan karancin kulawa a kan rashin kulawa da ake yi da su.
Tuni kasashen Larabawa suka suka yi alkawarin kawo gyara a aikin.
Ko a watan da ya gabata ma Qatar ta kawo wata sabuwar doka da ta ba wa ma'aikatan 'yancinsu da suka hada da a kalla a ba su hutun kwana daya a mako da kuma biyansu kudin hutu na shekara-shekara.
Masu fafutuka sun ce babban kalubalen shi ne aiwatar da wadannan sabbin dokoki, da kuma kaucewa irin wannan tsari da kara wasu dokoki ta inda sabbin dokokin zasu samu gindin zama.
Wata 'yar aiki ta shaida wa BBC cewa, 'yan aikin gidan sun sha guduwa suna neman aikin da ya saba ka'ida, sakamakon jinkiri wajen biyansu, da kuma cin zarafinsu da ake yi da kuma yin aiki a cikin yanayi mara dadi, kuma wadannan ma'aikatan suna da masaniyar cin kasuwar da ake yi a shafin intanet.
Wata mata da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, "Yanzu idan ka je ka cewa wani ina neman aiki, bisa ka'ida ko wanda ya saba ka'ida, mutum zai saka lambarka a irin wannan shafikan na Facebook, ta haka ne ake iya samun aiki a shafikan intanet ... amma kuma hakan ya saba ka'ida".
Source: BBC Hausa
Title :
Yadda Ake Cinikin 'Yan Aiki A Internet
Description : Batun ma'aikata 'yan cirani da ke aiki a kasashen Larabawa, ya dade ana cece-kuce akai, da kuma yadda ake kai su yin ayyukan, wanda ...
Rating :
5