Shugaba Donald Trump na Amurka ya nemi majalisar dokokin kasar ta ba shi kusan dala biliyan 8 a matsayin tallafin da za a taimaka wa wadanda bala'in ambaliya ya shafa a Texas.
A wasikar da ke kunshe da wannan bukata wadda aka gabatar ga kakaki majalisar wakilan Amurka, Paul Ryan, darektan kasafin kudi na fadar gwamnatin Amurka, Mick Mulvaney, ya ce da wuya a amince da wata bukatar karin wani kudin, har sai majalisar dokoki ta daga yawan ka'idar bashin gwamnati.
Wanda idan hakan bai samu ba, za a iya samun matsala ga kokarin sake daidaita al'amura a wuraren da bala'in ya afaka wa.
Bukatar kudin na daga kudirin Shugaba Trump na taimaka wa jihohin da bala'in ya fada wa, domin su samu su farfado, kuma wata bukatar kudi a nan gaba za ta kasance ta fadada aikin sake gina muhallai ce In ji Mista Mulvaney.
Darektan kasafin kudin na White House, ya ce kusan magidanta rabin miliyan ne suka yi rijista domin samun tallafin haya da kuma gyara muhimman kayan gidajensu.
Mummunar guguwar mai tafe da ruwa wadda ta fada wa Texas mako daya da ya wuce, ta haddasa mummunar ambaliya ruwa.
Wannan iftila'i, ya janyo mutuwar mutum akalla 47, tare da raba kusan dubu 43 da gidajensu inda a yanzu suka fake a sansanonin wucin-gadi.
Ana ganin kusan kashi 80 cikin dari na mazauna Texas ba su da inshorar ambaliya da za ta ba su damar gyara bannar da suka gamu da ita cikin sauki.
A yau Asabar ne dai Shugaba Trump zai sake ziyartar yankin a karo na biyu.
Source: BBC Hausa
Title :
Trump Na Neman Biliyan 8 Don Tallafawa Wandanda Ambaliya Ta Afka Wa
Description : Shugaba Donald Trump na Amurka ya nemi majalisar dokokin kasar ta ba shi kusan dala biliyan 8 a matsayin tallafin da za a taimaka wa wadanda...
Rating :
5