A ranar Alhamis 31 ga watan Agusta za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa ta Turai ta bana, wacce za a sake budewa a watan Janairun 2018.
Ana bude kasuwar ce domin bai wa kungiyoyin Turai damar daura damarar tunkarar kalubalen tamaula a sabuwar kaka.
Ga jerin cinikin ranar rufe kasuwar da aka yi takaddama a Premier:
Benjani
Dan wasan tawagar Zimbabwe, Benjani ya makara zuwa Etihad domin ya saka hannu kan yarjejeniyar komawa Manchester City, bayan da bacci ya kwashe shi a filin saukar jirgin sama na Southampton a Janairun 2008.
Makarar da dan wasan ya yi ya kusan sa a soke yarjejeniyar da aka kulla tun farko, daga baya aka warware matsalar bayan da aka kammala sa hannu a dukkan takardun da suka dace a kan kari.
Benjani ya fara buga wasa a City da kafar dama inda ya ci Manchester United a wasan hamayya da suka kara.
Daga baya dan kwallon ya kasa yin komai, hakan ya sa ya bar Etihad a shekarar 2010 bayan da ci kwallo biyar.
Yossi Benayoun da Mikel Arteta
Bayan da Arsenal ta sayar da Cesc Fabregas da kuma Samir Nasri ta samu kudi fam miliyan 60 a shekarar 2011, daga nan ne Arsene Wenger ya dunga jan lokaci kafin ya sayo wadanda za su maye gurbinsu.
Sai a ranar da za a rufe kasuwa ne Wenger ya sayo Benayoun da kuma Arteta, ya kuma sayo Arteka kan fam miliyan 10, inda ya yi shekara biyar a Gunners, shi kuwa Benayoun Chelsea ya koma wasa aro daga baya ba ta sayi dan kwallon ba.
Peter Odemwingie
Dan wasan Najeriya, Peter Odemwingie ya dauki hukunci a hannunsa a wani abu kamar almara da bai taba faruwa ba a Ingila, inda ya so komawa QPR daga West Brom da karfin tsiya a Janairun 2013.
Odemwingie ya tuka motarsa zuwa QPR daga West Brom, amma aka ce ya koma inda ya fito, saboda kungiyoyin biyu ba su kulla yarjejeniya ba, kuma tun da ya koma West Brom ba ta kara saka shi a wasa ba.
Rafael van der Vaart
Kocin Tottenham, Harry Redknapp ya matsu ya dauki Rafael van der Vaart daga Real Madrid a shekarar 2010.
Sai dai rashin kammala sa hannu kan yarjejeniya ya kusan hana dan kwallon komawa Ingila da murza-leda, amma daga baya mahukuntan Premier suka amince da cinikin bayan da aka rufe kasuwa.
Van der Vaart ya yi kaka biyu a White Hart Lane, inda ya ci kwallo 23.
Fernando Torres da Andy Carroll
Bayan da Liverpool ta amince ta sayar wa da Chelsea Fernando Torres kan fam miliyan 50 a ranar 31 ga watan Agustan 2011, Liverpool kuma a lokacin ta sayi Andy Carroll kan fam miliyan 35 daga Newcastle United.
An yi ta mamakin dalilin da ya sa Liverpool ta sayi Carroll kan kudi mai yawa haka, daga baya 'yan wasan biyu suka kasa taka rawar gani a kungiyoyin da suka koma.
A kuma shekarar ce Luis Suarez ya ci kwallo 69 a yarjejeniyar shekara uku da rabi a Anfield, amma ta sayar da shi ga Barcelona a kudi mai tsoka.
David Dea
Mai tsaron ragar Manchester United, David De Gea ya kusan komawa Real Madrid a ranar da za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a 2015.
Tuni United da Madrid suka amince da kudin da ya kusan kai fam miliyan 30, sai dai kungiyoyin biyu sun kasa cike takaddun ka'ida da ya kamata dan kwallon ya koma Spaniya da taka-leda, hakan ya sa suka hakura da cinikin De Gea.
Andrey Arshavin
A lokacin da za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan Turai a karshen Janairun 2009 ne Arsenal ta sayi Andrey Arshavin daga Zenit St Petersburg kan kudi mai tsada da ya kai fam miliyan 15.
An samu tsaiko wajen cimma yarjejeniyar kudin dan wasan, inda sai washe gari ne Arsenal ta fadi kudin da ta dauki dan kwallon.
Mahukuntan Premier sai da suka yi bincike ko Arsenal ta karya ka'idar sayen dan wasan, daga baya aka wanke ta.
Source: BBC Hausa
Title :
Takaddamar Cinikin Ranar Karshe Da Akayi A Premier
Description : A ranar Alhamis 31 ga watan Agusta za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa ta Turai ta bana, wacce za a sake budewa a watan...
Rating :
5