Wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, NBS, ta fitar ya nuna cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta fada.
Rahoton ya ce tattalin arzikin ya bunkasa da kashi 0.55 cikin 100 a rubu'i na biyu na shekarar 2017 idan aka kwatanta da rubu'i na biyu na shekarar 2016.
Hakan yana nufin cewa girman wannan bunkasa da aka samu ya haura wanda aka samu a rubu'i na biyu na shekarar 2016 da kashi 2.04 cikin 100.
Tattalin arzikin kasar ya samu wannan tagomashi ne bayan da ya kwashe rubu'i biyar yana ci gaba da tsukewa.
A lokacin da tattalin arzikin ya bunkasa, ana fitar da gangar danyen mai 1.84m a kowacce rana, in ji NBS.
Ta kara da cewa, baya ga man fetur, harkar noma da inshora da gas da lantarki na cikin abubuwan da suka taimaka wajen bunaksar tattalin arzikin.
Source: BBC Hausa
Title :
Nigeria Tafita Daga Matsin Tattalin Arziki
Description : Wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, NBS, ta fitar ya nuna cewa kasar ta fita daga matsin tattal...
Rating :
5