Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce ya yi jinkiri kan sake sanya hannu a sabuwar kwantaragi da kulob din a kakar wasan da ta wuce saboda yana ganin ba shi da kwarewar ci gaba da jagorantarsu.
A watan Mayu ne Wenger ya sanya hannu kan sabuwar kwantaragi, wata daya kafin tsohuwar kwantaraginsa ta kare.
Ya shaida wa wani gidan talabijin na Faransa mai suna Telefoot cewa wasu dalilai ne "na kashin kaina" suka sanya na jinkirta sanya hannu a sabuwar kwanrtaragi da kulob din da ya kwashe shekarar 21 yana jagoranta.
Sai dai ya kara da cewa: "Na jima ina jogorantar kulob din har ma aka yi tunanin anya zan iya ciyar da shi gaba?"
Kulob din na Arsenal na kammala kakar wasan Premier da ta wuce a matsayi na biyar - karon farko da suka kammala ba tare da kasancewa cikin hudun farko ba tun da Wenger ya soma aiki da su a 1996 - kafin su doke Chelsea inda suka dauki kofin FA.
Arsenal sun fara kakar wasa ta bana ne da yin nasara a kan Leicester da ci 4-3 a gida, kafin Stoke ta doke su da ci 1-0 da kuma cin da Liverpool ta yi musu 4-0.
"Na kwashe shekara da shekaru a Arsenal kuma a kakar wasan da ta wuce mun yi ta gwagwarmaya," in ji dan kasar ta Faransa mai shekara 67.
"A wasanmu na farko a kakar wasa ta bana mun yi nasara, ko da yake an ba mu kashi a wasa na biyu sannan mun yi faduwar bakar tasa a daya wasan.
"Amma yanzu za mu wartsake, kuma kamar yadda yake a duk lokacin da ake cikin matsala, kana bukatar cin wasanka na gaba."
Source: BBC Hausa
Title :
Nayi shakkar Iya Sake Jagorantar Arsenal-Wenger
Description : Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce ya yi jinkiri kan sake sanya hannu a sabuwar kwantaragi da kulob din a kakar wasan da ta wuce saboda yana ...
Rating :
5