Sallar Idin bana ta zo da sabon salo a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, yayin da Gwamnan Jihar Ayo Fayose ya bayyana a sahun gaba, a bayan liman daure da farin rawani da dogon carbi.
Fayose, wanda Kirista ne, an gudanar da Sallar Idin tare da shi. Jim kadan bayan kammala Sallah, Fayose ya bayyana wa manema labarai cewa, ba wannan ne karon farko da ya shiga sha’anin addinin Musulunci aka gudanar tare da shi ba.
Daga nan sai ya yi kira ga malaman Musulunci da su rika gaya wa shugabanni gaskiya, ko su so ko ba su so ba.
Fayose ya kuma yi kira da a guji rigingimu da kashe-kashe, inda ya furta cewa, “Musulunci ba addini da aka sani da tashin hankali ba ne.”
Source: BBC Hausa
Title :
Musulunci Ba Addinin Tashin Hankali Bane-Fayose
Description : Sallar Idin bana ta zo da sabon salo a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, yayin da Gwamnan Jihar Ayo Fayose ya bayyana a sahun gaba, a ba...
Rating :
5