Jose Mourinho ya ce, " kulob din Manchester United zai zama gagara-gasa duk da matsalolin da suka faru a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon.
A ranar Alhamis ne United ta yi fatali da kudirin da aka kawo a kan za a rufe kasuwar badi kafin a fara kakar wasannin Firimiyar 2018-19.
Mourinho ya ce, akwai rashin amfani yayin da aka rufe kasuwar saboda mu kuma a bude saboda wasu.
"Amma yayin da muka rufe kasuwarmu, to kenan mun rufe kasuwar wasu," in ji shi.
Dan Portugal din ya amince da kudirin da kulob din Firimiya 14 suka kada kuri'a a kai, mafi karancin abun da ake bukata na amincewa da shirin.
Ko da yake kulob dinsa da na Manchester City, da Watford, da Swansea da Crystal Palace duk sun yi fatali da kudirin, inda Burnley kuma ta zama 'yan ba ruwanmu.
Ya kara da cewa, "Ina so na isa a ranar farko tare da 'yan wasana, ba na son na bata lokaci wajen jinkirta shawarwari, wannan shi ne tunanin koci.
"Wannan shi ne dalilin da yasa United taki kada kuri'ar," in ji shi.
Source: BBC Hausa
Title :
Musayar 'Yan kwallo Bazata Shafi Kulob Ba-Mourinho
Description : Jose Mourinho ya ce, " kulob din Manchester United zai zama gagara-gasa duk da matsalolin da suka faru a rufe kasuwar saye da sayar da ...
Rating :
5