Ministar harkokin mata ta Najeriya ta soma yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar yakin neman zabe na shekarar 2019.
Hajiya Aisha Jummai Alhassan, wacce ta jagoranci shugabannin jam'iyyar APC na jihar Taraba domin kai gaisuwar Sallah ga Atiku Abubakar, ta yi addu'ar Allah ya ba shi shugabancin kasar a 2019.
Wani bidiyo da jaridar Daily Nigerian wacce ake wallafawa a shafin intanet ta buga, ya nuna ministar a gaban tsohon mataimakin shugaban kasar tana cewa, "Your Excellency (mai girma), babanmu, shugaban kasarmu idan Allah ya yarda a shekarar 2019... a gabanka, mutanenka ne, magoya bayanka har abada; mutanen jihar Taraba.
"Sun zo gaisuwar ban-girma, gaisuwar Sallah da kuma yi maka murna ta wannan daukaka (Wazirin Adamawa) da Allah ya kara maka".
Hajiya Jummai ta gabatar wa tsohon mataimakin shugaban kasar shugabannin jam'iyyar, tana mai cewa wasunsu sun matsa domin su yi jawabi a gabansa amma hakan ba zai yiwu ba saboda ya gaji.
Tawagar ta rika yin tafi a lokacin da ministar ke wadannan jawabai.
Ministar ta harkokin mata dai ita ce ta yi takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin jam'iyyar APC a shekarar 2015, ko da yake ta sha kaye a hannun Gwamna mai-ci, Darius Ishaku na jam'iyyar PDP.
Masana harkokin siyasa dai na ganin tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda ya fafata da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben fitar da gwani na APC a shekarar 2014, zai sake tsayawa takara a zaben 2019.
Suna ganin wannan ce dama ta karshe ga Atiku Abubakar ta zama shugaban kasar, ganin cewa har yanzu ana tunanin za a fitar da shugaban kasar ne daga arewacin kasar, sannan shekarunsa na ci gaba da ja, inda ya haura shekara 70.
Sai dai suna ganin zai fuskanci babban kalubale a wurin mutane irinsu su tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda ya zo na biyu a zaben fitar da gwanin na APC a wancan lokaci kuma ake tunanin zai sake son tsayawa takara, da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i, da kuma shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki, wadanda ake ganin za su yi takarar shugabancin kasar.
Kazalika masana siyasa na ganin Atiku Abubakar zai fuskanci adawa daga tsohon mai gidansa Cif Olusegun Obasanjo, wanda ake ganin ba sa ga-maciji da juna.
Sun bayyana cewa rashin lafiyar da Shugaba Buhari, mai shekara 74, ke fama da ita na cikin abubuwan da ke kara kaimi ga masu son yin takara a zaben 2019 su fito su bayyana hakan, alabishi idan ya ce ba zai sake yin takara ba.
Amma har yanzu shugaban bai bayyana shaukinsa na sake tsayawa takarar ba ko akasin hakan.
Amma makusantansa sun nuna yiwuwar tsayawa takararsa a shekarar 2019.
Source: BBC Hausa
Title :
Ministar Buhari Tafara Yiwa Atiku Kamfe
Description : Ministar harkokin mata ta Najeriya ta soma yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar yakin neman zabe na shekarar 2019. Hajiya...
Rating :
5