Likitoci a jihar Gujarat da ke yammacin Indiya sun yi nasarar cire wa wani jariri ɗan wata ɗaya haƙora guda bakwai a bakinsa.
"Jaririn a yanzu yana cikin ƙoshin lafiya," kamar yadda likitan hakori Dr Meet Ramatri, da ya gudanar da aikin a watan Agusta ya faɗa wa Sushila Singh ta sashen BBC Hindi.
Ya ce an gudanar da tiyatar cire hakoran ne cikin mataki biyu. Inda tashin farko suka zare wa jaririn haƙori huɗu, daga bisani kuma aka cire sauran uku.
An gano haƙoran rakwacam a bakin wannan jariri ne kwanaki ƙalilan bayan haihuwarsa.
Iyayensa sun kai shi wajen likitan jarirai, bayan sun fuskanci yadda ɗansu ke shan wahala wajen shan nono.
Da ya bincika, sai likitan ya gano wani farin tantakwashi a bakin jaririn, don haka ya tura iyayensa wajen Dr Ramatri.
"Da na duba shi, na gano haƙori bakwai a cikin bakinsa," Dr Ramatri ya fada wa BBC Hindi.
"Wasu lokuta za ka ga ɓullowar 'yan haƙora haka a bakin jariri sabuwar haihuwa, amma dai ba cikakkun hakora ba ne kamar na manya a wannan lokaci.
Sai dai a wannan karo, haƙoran wannan jariri sun fito sosai."
Yayin da Dr Ramatri ke cewa bai taɓa karanta wani abu makamancin haka ba a baya, amma dai yana jin cewa ba lallai ne ya kasance wani abin ba sabon ba.
Ala dole ya cire wa jaririn haƙoran ta hanyar tiyata, kamar yadda ya ce.
"Saboda ba su kafu sun yi karfi ba, idan da ɗaya a cikinsu ya karye, da ya shigewa jaririn maƙoshi, hakan kuma ba ƙaramin hatsari ba ne."
A yanzu jaririn na iya shan mama, in ji likita, sai dai ya ƙara da cewa da wuya a iya gane ko tiyatar da aka yi masa ka iya zama cikas ga fitowar wasu haƙoran a nan gaba.
Source: BBC Hausa
Title :
Likitoci Sun Gaggabe Ma Wani Jariri Hakora
Description : Likitoci a jihar Gujarat da ke yammacin Indiya sun yi nasarar cire wa wani jariri ɗan wata ɗaya haƙora guda bakwai a bakinsa. "Jaririn...
Rating :
5