Kwararru sun ce sun ji alamun wani motsin kasa mai karfin gaske a Koriya ta Arewa, abin da ya sa suke zargin cewa kila kasar, ta yi gwajin wani makamin nukiliya ne a karo na shida.
Motsin kasar wanda ya kai girman lamba 6 da digo 3 a ma'aunin girgizar kasa, kwararrun China da Amurka na zargin cewa wani gwaji ne na makamin kare dangi ya haifar da shi.
An kara jin wani motsin kasar bayan wasu 'yan mintuna da jin na farko.
Duka wannan dai ya faru ne 'yan sa'o'i bayan da Koriya ta Arewar ta ce ta hada wani babban bam wanda za a iya makala shi a jikin makami mai linzami da za a iya harba shi daga nahiya zuwa nahiya.
Wannan motsi da masanan suka gano ya kasance wani lamari da zai iya kara tayar da hankalin kasashen da ke kallon hadarin-kaji tsakaninsu da Koriya ta Arewa.
'Yan sa'oi da kasashen suka shiga laluben yadda za su bullo wa maganar rahoton da ke nuna Pyongyang din ta kirkiro bam din kare dangi, sai kuma ga batun gwajin da ya motsa kasa ya taso.
Kasa da mako daya bayan da ta yi wani gwajin makami mai linzami, Koriya ta Arewar ta ce ta kera wani babban makamin kare dangi.
Daman tuni Pyongyang din ta yi gwajin wani makamin roka mai linzami mai cin dogon zango, kuma masana da dama sun yi amanna, a gwajin tana sanya Amurka ne a zuciyarta, ta yadda idan har ta harba shi, ba zai fadi a ko'ina ba sai cikin tsakiyar Amurka.
Ana ganin idan har Koriya ta Arewar ta kai ga samun fasahar makala wa wannan makami mai linzami mai cin dogon zango, bam din kare dangi, to hakan wata babbar barazana ce ga Amurka.
Jim kadan bayan da Koriya ta Arewar ta fitar da wannan sanarwa shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana da Fraiministan Japan Shinzo Abe, kuma dukkaninsu sun amince cewa akwai bukatar kasashensu su hada kai da Koriya ta Kudu, su san yadda za su bullo wa wannan barazana ta Koriya ta Arewa da kulllum take karuwa.
Source: BBC Hausa
Title :
Korea Ta Arewa Ta Gwada Makamin Daya Motsa Kasa
Description : Kwararru sun ce sun ji alamun wani motsin kasa mai karfin gaske a Koriya ta Arewa, abin da ya sa suke zargin cewa kila kasar, ta yi gwajin w...
Rating :
5