A yau Juma'a ce al'umar Musulmi a fadin duniya ke bikin sallar layya, wadda aka fi sani da babbar sallah.
Bayan saukowa sallar idi ne ake yanka dabbobi ga wadanda ke da sunkuni.
Ana kuma sada zumunci da yawaita ayyukan neman lada.
Ibrahim Isa ya tattauna da Sheikh Ibrahim Khalil, shugaban majalisar malamai ta jihar Kano a kan abubuwan da aka kwadaita waMusulmi su yi a wannan rana, amma ya fara ne da bayani a kan muhimmancin ranar Idi:
Source: BBC Hausa