Daukar hoton a wuraren ibada abu ne da mutane suke yawan yi kuma su wallafa hotunan a shafukan sada zumunta na zamani inda abokansu za su gani su kuma yi tsokaci ko magana ko kuma yayata hoton.
Ba sabon abu ba ne mutun ya dauki hoto a masallacin idi ko na harami a Makka ko Madina ko kuma a filin Arfa.
Bugu da kari wasu na daukar hotuna na bidiyo a lokacin dawafi ko kuma lokacin hawa Arfa kuma su wallafa a shafukan sada zumunta na zamani.
Wata kila wasu na yin hakan ne domin su nuna wa duniya cewa sun samu zuwa wannan waje, yayin da wasu kuma suna son su nuna wa wadanda suke gida yadda wurin ibadar yake ne.
To amma wani lokacin hakan ba ya rasa nasaba da aikin riya da Musulunci ya hana.
Irin wannan dabi'ar ta samo asali ne tun zamanin da, inda mahajjata ke dawowa gida da kallo-kallo daga aikin hajji inda yara da sauran mutane da ba su samu zuwa aikin hajji ba za su samu ganin wuraren aikin hajji ta hotunan da ke cikin kallo-kallon.
Riya ce?
Wasu na tunanin cewar daukar hoto a irin wadannan wuraren ibadan son a-sani ne, wato riya ce. Amman mene ne hukuncin irin wannan dabi'ar a Musulunci?
Ustaz Hussaini Zakariya, ya ce, "Maganar daukar hoto idan aka je Harami ko Madina, malamai sun rabu gida biyu kan wannan batu."
"Daya mai tsanani kwarai da gaske, shi yana ganin cewa hoton ma haramun ne a ko ina aka yi, ba sai lallai cikin Harami ba, kuma yi a cikin Haramin ma ya fi muni."
"Amma akwai wadanda suke ganin cewa daukar hoto ba aikin ibada ba ne. Ba wanda zai dauki hoto ya ce ya yi sunnah ko mustahabi ko kuma ya yi farilla."
Malamin ya kara da cewa: "Don haka ba aikin ibada ba ne balle a ce in ka yi jama'a sun gani, aikinka ya baci. Don haka yana ganin cewa halal ne matukar dai mutum ba wai ya yi wannan abin don jama'a su ga cewa yana wajen wata ibada kuma burinsa ya cika ba ne."
"Ya kwadaita wa wadanda Allah bai ba su ma su roki Allah Ya kai su wannan wurin, kuma ya sanar da danginsa da abokansa cewa ga shi Allah Ya kawo shi wurin da duk Musulmi yake son ya zo."
"Ina ganin wani abu ne na raba abin farin cikin da ya samu mutum da 'yan uwansa da abokansa."
Saboda haka Ustaz Zakariya ya ce yana ganin wannan ba aikin addini ba ne kuma ba riya ba ce.
Source: BBC Hausa
Title :
Hukuncin Daukan Hoto A Gun Ibada
Description : Daukar hoton a wuraren ibada abu ne da mutane suke yawan yi kuma su wallafa hotunan a shafukan sada zumunta na zamani inda abokansu za su ga...
Rating :
5